✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya sumar da wata da mari a Abuja

Sojan ya dalla mata mari sai da ta suma, saboda ta tsallake wani shinge da sojoji suka saka

Wani soja da ke sa ido a kantin zamani na Banex Plaza da ke a Abuja ya stinke wata mata da mari sai da ta suma, saboda ta tsallake wani shinge da suka saka.

Sojoji sun rufe Banex Plaza ne saboda wasu da ake zargin zauna gari banza ne sun lakada wa wasu sojoji duka saboda sabanin da ya shiga tsakaninsu da wani dan kasuwa.

Wakilinmu ya je yankin domin sanin inda aka kwana bayan faruwar lamarin na ranar Asabar da ya jefa kasuwar da ’yan cikinta a mawuyacin hali.

Ana tsaka da hakan ne wata mata ta tsallaka wani shinge da sojoji suka saka.

Iya abin da wakikinmu ya iya hange shi ne sojojin sun yi wa matar tambayoyi.

Ana tsaka da haka sai wani daga cikin sojojin ya shinfide matar da mari.

Nan take ta zube a kasa sumammiya, abin da ya sa aka debe ta a ka saka a wata mota aka tafi da ita cikin hanzari.

Da yake mayar da martani game da lamarin a ranar Talata, kakakin Rundunar Sojin Kasa  ta Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa an rufe kasuwar ne na wucin gadi domin a kamo wadanda suka haddasa rikicin.

Manjo-Janar Nwachukwu ya ce yana da kyau a lura cewa sojojin da aka lakada wa dukan ba su dauke da makami kuma ba su aikata wani abu na wuce gona da iri da ke barazana ga wani ba.

Ya kara da cewa, zaluncin da aka yi musu bai dace ba, kuma “Har yanzu ba a kamo wadanda suka haddasa rikicin na Banex Plaza ba.

“Lamarin na bukatar a zurfafa gudanar bincike a wurin da abin ya faru, don gano musabbabin faruwar lamarin.

“Ana sa ran a karshe binciken zai tabbatar da tsaro a Abuja da kuma hana faruwar irin haka a nan gaba ga sojoji da sauran  jami’an tsaro, kamar yadda aka gani a wasu wurare,” in ji Nwachukwu.

Babban jami’in sojan ya yi kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen mu’amala da sojoji da sauran jami’an tsaro, musamman a lokacin da suke cikin kaki.

Ya ce akwai hanyoyin da za a iya kai karar sojoji idan sun yi wani laifi ko rashin da’a ga hukumomin da suka dace.

A cewarsa, ya zama wajibi a yi amfani da wadannan hanyoyi wajen tabbatar da zaman lafiya da mutunta masu yi wa al’ummarmu hidima.