Iyayen wani matashi da ke aiki a Asibitin Rundunar Sojin Sama da ke Kano sun zargi wani soja da kashe dan nasu.
Jama’ar unguwar Gwagwarwa da ke Karamar Hukumar Nasarawa suna zargin wani sojan sama da ake kira Oga Aminu ne ya kashe matashin mai suna Yusuf Shuaibu.
Mahaifin Yusuf, mai suna Malama Shuaibu Bala, ya bayyana cewa Oga Aminu ne ya gantsara wa dan nasa cizo, har rai ya yi halinsa.
Malama Shuaibu, ya bayyana cewa dan nasa ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake shirin dawowa gida.
- Kotu ta ɗaure tsohon manajan banki shekara 121 kan zambar kuɗi
- Mutumin da ya shuka itatuwan kuka 3,000 cikin shekara 47
Ya ce, “Yusuf ya tashi daga aikin dare zai dawo gida ne Oga Aminu ya sa shi wani aiki.
“Bayan ya kammala aikin ne ya bukaci kudin abinci, shi ne shi kuma Oga Aminun ya kai masa farmaki, har ya cije shi, hari wurin ya yi rauni.”
Malam Shuaibu ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam da kuma Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshal Hassan Abubakar, su bi musu hakkin dansa.
Mai magana da yawun Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya ce babban hafsan rundunar, ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin.
A sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, Gabkwet ya ce an gano cewa a baya-bayan nan Yusuf sun samu hatsaniya da sojan kuma an shiga tsakani aka sasanata su.
Amma ya ce duk da haka ana kan gudanar da bincike don gani ainihin musabbabin rasuwar matashin.