Wani sojan Najeriya ya harbe kansa bayan an gano shi cikin mayakan Boko Haram da ISWAP da suka kai harin bom a Jirhar Yobe.
Dubun sojan, wanda ke aiki a Gaidam na jihar ta cika ne bayan musayar wutar da sojoji suka yi da ’yan ISWAP da suka kai hari a wata mashaya suka kashe mutum tara.
- Bazaranar tsaro: An rufe Kasuwar Mammy da ke Damaturu
- NAJERIYA A YAU: Za A Kai Wa Wuraren Ibada Harin Bom —DSS
Jami’in leken asirin nan, Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Yankin Tafkin Chadi, ya saida wa ’yan jarida cewa an fara zargin sojan ne bayan ya yi batar dabo daga bakin aikinsa na kwana biyu.
Majiyar ta bayyana cewa a ranar 21 ga watan Afrilu, an ga sojan a cikin ’yan ta’addar da suka kai hari a wata mashaya a garin Gaidam tare da kashe mutane kusan tara.
Ya ce “Saboda haka kwamandansa, Laftanar Kanar Mikah, ya bi diddigin wayarsa, aka gano shi a garin Gashua na Karamar Hukumar Bade, mai nisan kilomita 105 daga Geidam.
An kai hari kan wata mashaya a garin na Gashua dab da lokacin danke shi, inda aka kashe mutum daya, wasu bakwai suka jikkata.
An yi imanin cewa sojan mai mukamin Las Kofur daya ne daga cikin wadanda suka tsara kai harin,” inji majiyar.
Ta bayyana cewa nan take aka tura sako zuwa sansanin sojoji da ke Gashua aka yi mishi kofar rago ta hanyar binciken kwakwaf.
Ranar Talata da safe ya yi kokarin ya shiga wata motar bas zuwa Gombe amma aka gano shi aka kama shi a shingen binciken ababen hawa a Gashua.
Bayan an kama shi an daure shi a hanyar kai shi Geidam ne ya yi amfani da kwarewarsa ta mai koyar da dabarun sarrafa makami, ya kwace bindigar daya daga cikin masu rakiyarsa, ya ci karfin daya kuma ya tarwatsa kansa da bindigar.
Majiyar ta bayyaan cewa bayanan da Jubrin ya yi kafin ya halaka kansa sun kai ga kama wasu ’yan uwansa sojoji masu hanu a ayyukan ta’addanci.
Majiyar ta Zagazaola ta ce Jubrin yana Sashen Leken Asiri ne kafin daga bisani ya zama malamin koyar da dabarun sarrafa makamai a rundunar ta soja.