Wani jami’in Hukumar Kwastam ya yi gamo da ajalinsa yayin da wani soja ya harbe shi a iyakar kan tudu ta Seme da ke Jihar Legas.
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare.
- An nada Mukaddashin Shugaban Hukumar NECO
- Yadda za a magance rashawa a Najeriya — Shugaban Media Trust
“Da yiwuwar sojan yana cikin maye ne na barasa don babu wanda ya taba tsammanin zai yi aikata wannan barna da ba a san shi da ita ba,” a cewarsa.
Seme yanki ne na kasar Najeriya da ke iyaka da Kwatano, babban birnin Jamhuriyyar Benin.