✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya harbe DPO ɗin ’yan sanda a Zamfara

Duk da cewa ya bayyana musu cewa shi ɗan sanda ne kamar yadda suka buƙata amma sai kawai wani soja ya zaro bindiga ya harbe…

Rahotani na cewa wani soja ya sa bindiga ya harbe wani DPO ɗin ’yan sanda a wani shingen binciken ababen hawa a Jihar Zamfara.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce lamarin dai ya faru ne a garin Ɗanmarke da ke karƙashin Ƙaramar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara da misalin ƙarfe 10:30 na ranar Laraba.

SP Halliru Liman wanda shi ne DPO na Wasugu da ke Jihar Kebbi ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa ta halartar taronsu na wata-wata, inda sojojin da ke ƙarƙashin rundunar Hadarin Daji suka tsayar da shi a wani shingen bincike.

“Duk da cewa ya bayyana musu cewa shi ɗan sanda ne kamar yadda suka buƙata amma kuma sai kawai wani soja mai suna Hassan ya zaro bindiga ya harbe SP Liman a kansa, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa,” in ji sanarwar.

Rundunar ’yan sandan ta Jihar Zamfara ta nemi da dukkan hukumomin da ke da ruwa da tsaki da su gudanar da cikakken bincike na yadda al’amarin ya faru.

“Abin da sojojin suka yi ya fito fili da irin rashin son aiki tare da sauran jami’an tsaro wanda kuma ba za mu lamunta ba,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.