✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasar Kano: Taron Shekarau da wasu jiga-jigan APC ya tada kura

Taron ya sanya shakku a zukatan wasu 'ya'yan jam'iyyar APC a Kano.

Taron da ’yan Majalisar Dattawa daga Jihar Kano suka yi a gidan tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekaru ya yamutsa hazo, tare da alamta irin rikicin shugabancin da jami’iyyar ke ciki a jihar.

Sanatocin da wasu ’yan Majalisar Tarayya sun yi zaman ne a ranar Asabar din da ta gabata a gidan Shekaru da ke Abuja, a yayin da zaben shugabancin jam’iyyar da za a gudanar yake karato.

Shekarau, wanda ya mulki Jihar Kano sau biyu a jere, kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a yanzu, ya karbi bakuncin Sanata Kabiru Gaya (Kano ta Kudu) da Sanata Barau Jibrin (Kano ta Arewa) a gidansa nasa.

Sauran mahalarta sun hada da dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Birni, Sha’aban Ibrahim Sharada; dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa/Rimin Gado, Tijjani Jobe; dan majalisa mai wakiltar Karaye/Rogo, Haruna Dederi; da kuma dan majalisa mai wakiltar Gabasawa/Gezawa, Nasiru Auduwa.

Halartar taron da daya daga cikin ’yan takarar shugabancin jam’iyyar ta APC a Jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Danzago, ya haifar da kumfar baki.

– Rikicin Ganduje da wasu –

Masu masaniya game da abin da ke faruwar a jihar na hasashen cewa taron wani yunkuri ne na yin tawaye ga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Daga cikin mahalarta taron, Sharada da Jobe sun yi kaurin suna wajen suka tare da nuna wa gwamnan yatsa.

A bangare guda kuma yawan ganin shugaban jam’iyyar mai ci a jihar, Abdullahi Abbas, tare da Ganduje musamman a wajen taruka, ya sa wasu ke ganin yana da goyon bayan gwaman da kuma gagaruwar damar sake lashe zaben shugabancin jam’iyyar da za gudanar.

Amma Danzago ya shaida wa Aminiya cewa ya hadu da ’yan majalisar ne domin neman goyon bayansu a matsayinsa na mai neman kujerar shugabancin jam’iyyar a jihar.

– Bangaren Sanata Shekaru –

Mashawarcin Shekarau kan harkokin yada labarai, Sule Ya’u Sule, ya ce babu wani sabon abu a ganawar da ’yan majalisar suka yi a gidan mai gidansa.

Ya ce ’yan majalisar sun saba haduwa a gidan tsohon gwamnan lokaci zuwa lokaci, inda suke tattauna muhimman batutuwa da suka shafi jihar.

Sai dai wani tsagi na magoya bayan Shekarau sun bayyana cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin tsohon gwamnan da Ganduje.

Sun kuma yi zargin cewa a halin yanzu ba a kyautata musu duk kuwa da irin gudummawar da suka ba wa Gwanduje wajen lashe zaben 2019.

Masu sharhi kan siyasar Kano dai na ganin taron na iya zama wata alama ko manuniya game da makomar jam’iyyar, bayan kammala zaben shugabancinta da za a gudanar a ranar Asabar.