✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC a Kano: Shugaban Karamar Hukumar Birni ya rusa aikin Sha’aban Sharada

Shugaban Karamar Hukumar Birni ya rusa wurin ginin bisa zargin Sharada da yin kutse a filin gwamnati

Rikicin siyasar Jihar Kano tsakanin bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da Dan Majalisar Wakilai, mai wakiltar Karamar Hukumar Birni, Honorabul Sha’aban Sharada, ya dauki sabon salo.

A ranar Talata ce Shguaban Karamar Hukumar Birni, Hon. Fa’izu Alfindiki, ya jagoranci rusa wani aikin ginin cibiyar koyon sana’a wadda Hon. Sha’aban Sharada ke yi a mazabarsa da ke karamar hukumar.

Bidiyon da aka yada ya nuna Hon. Fai’zu alfindiki yana jagorantar wasu matasa da ke rusa ginin na Sha’aban Sharada, bisa zargin dan majalisar da yin kutse ko kwacen filin gwamnati.

Wani ganau ya ce, “Shugaban Karamar Hukumar Birni ne ya fara rusa allon shaidar aikin ginin, daga baya matasan suka taya shi rusa ginin. Sha’aban ya so ya gina wa jama’ar mazabarsa wurin koyon sana’a ne a wurin.”

Bayan rusa ginin ne jama’a suka yi ta ce-ce-ku-ce, inda wasu ke danganta hakan da bi-tada-kulllin siyasa.

Wani dan kasuwa a Sharada Kwanar Kasuwa, Nura Musa Aliyu, ya ce, “Abin takaici ne. Sha’aban ya zo ya same mu cewa zai gina wurin. Ya kuma yi alkawari cewa mu da ke kasuwnci a wurin, zai sama mana wani wuri kuma shi zai biya.

“Mun yi murna da jin hakan kuma mutanen Sharada sun yi na’am da aikin; kwatsam kuma jiya da yamma sai ga shugaban karamar hukuma ya zo ya rusa komai,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin yankin, Kamal Abdullahi, ya ce, “Aikin abu ne da zai amfane mu kai tsaye ko a kaikaice, ba mu kadai ba har da wadanda za a haifa nan gaba.

“Mun san dai ko ba dade, ko ba juma, sai an yi amfani da wannan wurin. Amma wane amfani za a yi da shi? Abin da ba mu sani ba ke nan.”

– Kwacen filin gwamnati

Amma a bayaninsa, Alfidiki ya ce Sha’aban Sharada, “Ba shi da izinin yin ginin daga Hukumar Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA),  hasali ma bai tuntubi Gwamnatin Jihar Kano game cewa zai yi ginin ba.

“Muna da dokokin da ka’idojin amfani da filaye da yin gine-gine, amma bai bi su ba. So dai kawai yake ya goga wa gwamnatin jihar kashin kaji a idon jama’a.

“Filin mallakin Gwamnatin Jihar Kano ne kuma ba sayen filin Sha’aban ya yi ba, ballantana ya samu izinin gini daga Karamar Hukumar Birni.”

Idan ba a manta ba a watan Oktoba, gabanin taron zaben shugabannin jam’iyyar APC, dangantaka ta yi tsami tsakanin ’yan Majalisar Jihar Kano hudu a matakin tarayya, karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau da bangaren Gwamnan Ganduje da ke goyon bayan sauran ’yan majalisar.

A lokacin ne bangaren Shekarau da Sharada da sauran ’yan majalisar suka kai wa uwar jam’iyyar APC kara suna zargin bangaren Gwamna Ganduje da haddasa tsahin-tashina a reshen jihar Kano.