Mai horar da ’yan wasan kwallon kafa na kungiyar Gombe United, Aliyu Zubairu, ya koka kan yadda wadansu korarrun shugabanin kungiyar ke tsoma baki da sanya siyasa a harkar tafiyar da kungiyar don gurgunta ta.
Kocin Aliyu Zubairu, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya ta waya cewa kulob din Gombe United bai da matsala da gwamnati wajen biyansu hakkokinsu da na ’yan wasa, amma tsofaffin shugabannin da aka kora su ne suke kawo tarnaki da matsala a harkar tafiyar da kungiyar.
Ya ce a matsayinsa na koci mai horar da ’yan wasa ci gaba yake ta kokarin ganin kawo wa kungiyar amma marasa kishi na yi masa zagon kasa.
A cewarsa kwanakin baya da kulob din ya yi nasara a filin wasa na Pantami, maimakon a taya su murna sai wadancan mutane suka yi ta kokarin su doke shi sai da jami’an tsaro suka raka shi mota da kyar.
Aliyu Zubairu, ya yi kira ga masu korafi cewa idan kishin Gombe da kulob din ne a ransu su, to ya kamata su yi hakuri a kai kulob din matakin da ya dace.
Ya jinjina wa shugabannin da suke rike da kungiyar a yanzu inda ya ce suna da kwazo da kishin jihar wanda hakan ya sa suke ta kokari don gani kungiyar ta ci gaba da samun nasara, amma shugabanin da aka kora kafin zuwansa su ne matsalar kulob din a halin yanzu.
Daga nan sai ya ce wasan da kungiyar za ta buga anan gaba da Yobe Dessert a garin Damaturu a ranar 10 ga Janairu su ne za su yi nasara in Allah Ya yarda.