Assalamu alaikum; barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
A wannan makon insha Allah za mu gabatar da bayani ga uwargida ce kan yadda za ta mori zama da maigidanta da kuma iyalinta.
- EFCC ta saki tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai Patricia Etteh
- IPOB: ’Yan bindiga sun fille kan dan majalisa a Anambra
Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.
Makiyan ainihi: Duk macen auren da za a tambaya ta lissafo manyan makiyanta na gidan duniya, zai yi wuya a ji ta kirgo da su a ciki, alhali kuwa su ne mafiya munin makiya!
Domin in har ta yi sakaci, su ne za su zama sanadiyyar rashin dacewarta da babban rabo a Ranar Lahira.
Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana su wane ne makiyanmu na ainihi a cikin Littafinsa Mai girma: “Ya ku wadanda suka yi imani! Lallai daga cikin ma’auratanku (matan aurenku ko mazan aurenku) da ’ya’yanku akwai makiyya a gare ku; sai ku kiyaye su.” (Suratul Taghabun, Aya ta 14).
Don haka ki sani yake uwargida! Maigidanki da kike so, kika bai wa muhimmanci sama da kowa da ’ya’yanki da kike ji da su kika daukaka jin dadinsu sama da naki, su ne makiyanki na ainihi!
Duk da cewa ba su kin ki a zuciyarsu kuma ba su yi maki mummunar fata, amma a fakaice manyan makiyanki ne, domin in kika yi sake sai su ja maki asarar da wani bayyanannen makiyin naki ma bai ja maki ba, wannan kuwa shi ne rashin dacewa da babban rabo Ranar Lahira.
Don haka, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya umarce ki da ki kiyaye su, sai ki kiyaye yake ’yar uwa domin wannan ne babbar gatar da za ki yi wa kanki da su iyalan naki.
Lakanin da zai ba ki galaba a kan makiyanki: Lakani daya ne zai ba ki cikakkiyar galaba ga makiyanki a duniya da Lahira, wannan lakani mai tsananin girma ne, mai saukin aikatawa kuma mai tsananin tasiri ga samun nasarar rayuwa a duniya da Lahira.
Wannan lakani shi ne riko da Allah shi kadai ba tare da hada shi da kowa ko komai ba; riko da Allah ya kunshi sa Allah a gaba, da ba Shi muhimmanci a zuci da aikace sama da komai a cikin rayuwa; ta yadda Shi kadai za ki bi a cikin dukkan al’amuran rayuwarki; wato ba za ki bi son ranki ba, ko son ran maigidanki ko na ’ya’yanki; Allah kadai kikasa a gaba kuma Shi kadai za ki bi.
In kika dawwama cikin aikata haka ya ’yar uwa, tabbas Allah Madaukakin Sarki zai ba ki kariya daga sharrin wadannan makiya naki, zai daukaka ki a rayuwarki kuma ki bar ambato mai kyau a bayan mutuwarki, zai ba ki mikakkiyar daraja daga duniya har Lahira.
Wannan shi ne babban lakanin samun galaba ga makiyanki; sauran bayani da zai zo duk yana kara nanata wannan babban lakanin ne.
Yadda za ki zauna da su: Bayan Allah Ya bayyana mana ko su wane ne makiyanmu na ainihi, kuma bai bar mu haka nan ba Subhanahu Wa Ta’ala, sai da Ya sanar mana mafiya kyan hanyoyin da za mu mu’amalance su don ya kasance ba su zama sanadiyyar halakarmu a rayuwar duniya da Lahira ba; inda Ya ce: “Kuma idan kun yi afuwa, kuma kuka kau da kai kuma kuka gafarta, to lallai Allah Mai gafara ne Mai jinkai.”
Wadannan sinadarai uku: afuwa; kau da kai da kuma gafara su ne sinadaran kyakkyawar dangantaka.
In kika yi la’akari ya ’yar uwa za ki fahimci cewa duka wadannan sinadarai suna umartarki da abu daya ne kawai: wato yadda za ki saukaka mu’amalarki da su.
Don haka ga bayani kan yadda za ki yi amfani da wadannan sinadarai wajen saukaka mu’amalarki da wadannan mafiya muhimmanci mutane gare ki.
Zan dakata a nan sai mako na gaba in Allah Ya kai mu, za mu dora da ga inda muka tsaya da yin addu’ar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin