✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sinadaran kamalar ’ya mace (7)

Assalamu alaikum.  Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.…

Assalamu alaikum.  Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga misalan da’a ga miji daga mata magabata.  Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Daga cikin abubuwan da suke kyautatawa da cika kamalar ’ya mace bayan kasancewarta salihar baiwa ga Ubangijinta akwai zama salihar mata ga mijinta. Manzon Allah (SAW) ya bayyana  salihar mace ga miji a cikin mafifita abubuwa daga cikin dadadan abubuwan duniyar nan. To in wani zai ji dadi da salihancin uwargida ai ba kamar ita da salihancin yake like da ita ba, kuma ya zagaye ilahirin kasancewarta. Mata magabata da suka yi zarra wajen yin cikakkiyar da’a ga mazan aurensu. Nana Asiya duk da kasancewar mijinta kafiri ne ta kasance mai yi masa da’a don takan zabi kalmomi wajen magana da shi kuma ta furta su cikin siga mafi dacewa har zuwa lokacin da aka aiko Annabi Musa (AS) da Manzanci sannan ta barranta da mijinta ta zabi sakon Annabi Musa.

Haka kuma tsananin da’a da karrama miji irin Nana Khadija  (RA) ba ya misaltuwa. Da sauran duk matan Annabi (SAW) iyayen Muminai (Allah Ya kara yarda da su).

Nana A’isha (RA) saboda tsananin da’arta mijinta Manzon Allah (SAW) ta hanyar rantsuwarta kadai yake gane bambanci in tana fushi da akasin haka. Ku dubi wannan tsananin girmamawa, ba ta canja fuska, ba ta kin yi masa dukkan hidimar da ta saba yi masa sai dai iyaka in ta tashi rantsuwa sai ta canja sunansa ta sa sunan Annabi Ibrahim. A wannan zamanin wata in tana fushi da mijinta, ba shi kadai ba ma kowa da ke hulda da ita sai ya sani. Haka nan an tambayi Nana A’isha (RA) wace matar aure ce mafificiya cikin matan aure?

Sai ta ce ita ce wadda ba ta san fadin bakaken maganganu ba, sannan ba ta da wayo irin na maza; abu daya ta sa a gaba shi ne gyaran jinkinta da yin kwalliya don mijinta da kuma kula da gidanta da iyalinta.

Sahabiyar Manzon Allah (SAW), Asma’u bint Abubakar (Radiyallahu Anha) ta ba da labari kamar haka: “Lokacin da Zubair ya aure ni, ya kasance bai da gona, kuma bai da dukiya ko bawa ko wani abu makamancin haka, sai rakumi don debo ruwa da kuma doki. Na kasance ina kai dokinsa wajen kiwo, in ba shi dusa, in kula da shi kuma in nika dabino don rakuminsa.Bayan haka kuma ina kai rakumin wajen kiwo, in yi hada-hadar sama masa ruwan sha, in dinke gugar jan ruwan sannan in kwaba gari. Ban iya gasa burodi ba sai dai makwabtana ke gasa mini sun kasance masu kirki. Sannan na kasance ina dauko wa bisa kaina kwallon dabino daga gonar Zubair wacce Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba shi mai nisan mil 2 daga Madina.

Wata rana ina dauke da kwallon dabinon, na gamu da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya kira ni kuma ya umarci taguwarsa ta rusuna don in hau, sai na ji kunya in yi tafiya cikin gungun maza musamman da na tuna irin  kishin Zubair, don ya kasance mutum mai tsananin kishi. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fahimci kunya nake ji sai ya wuce abinsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Sai na zo ga-Zubair na labarta masa duk abin da ya faru, sai ya ce “Wallahi, tunanin kin yi dakon ’ya’yan dabino ya fi mini ciwo fiye da hawa rakuminsa (Sallallahu Alaihi Wasallam).  Na ci gaba da rayuwa cikin wannan tsananin har sai da Abubakar (mahaifinta Radiyallahu Anhum) ya aiko mini da baiwa wacce ta daukar wa ranta kula da dokin sai na ji kamar ta ’yanta ni.

Darasin dauka ga uwargida shi ne ka da asalinta da ya fi na mijinta, ko kudinta ko yawan albashinta da ya fi na mijinta, ko wani matsayi, daukaka ko fasaha da take da shi da ya fi na mijinta ya sa ta rika ji ta fi karfin ta yi masa girki ko ta wanke masa kaya ko kawo masa abinci in dai har da gaske tana son zama Musulma tagari. Dubi dai wannan labari na Asma’u bint Abubakar, mahaifinta  Sayyidina Abubakar (Radiyallahu Anhu), bayan kasancewarsa babban sahabin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), mafifici a cikin mutane gaba daya in ba Annabi  (SAW) ba; kuma ya kasance mawadaci, ta girma cikin wadatar mahaifinta amma wannan bai sa ta kasa hidima ga mijinta ba, bayan aikin gida da take har na gona da kula da dabbobinsa tana yi. Amma a wannan lokaci wata ma ba ’yar kowa ba ce amma saboda ilimin boko da wayewa sai ta ji tana jin nauyin yin dan karamin aiki ga maigidanta. Lallai matan aure ku tashi tsaye ku sake daura damara, ku cire girman kai, ku yaki Shaidan, burinsa ya kange ku daga more rayuwar aurenku, karshe  ku rasa ladar yin ladabi da biyayya ga maigida, wato gidan Aljannar ni’ima. Allah Ya datar da mu duka, amin.

Sai mako na gaba insha Allah.   Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin