Duk da karuwar dimbin ribar da kamfanonin siminti suke samu a kasar nan, farashin simintin yana ci gaba da hauhawa a wata 18 da suka gabata.
Hakan ya faru ne duk da tabbacin da masana’antun ke bayarwa na cewa suna kara habaka samar da simintin.
- Yadda Najeriya ta ciyo bashin tiriliyan N2.5 a wata uku
- Ayyana dokar ta-baci kan matsalar tsaro babu amfani —Dingyadi
Tashin farashin simintin yana haifar da tsadar yin gini da sauran kayayyakin gine-gine.
Kamfanoni uku ne suke yin siminti a Najeriya wato Dangote da Lafarge (Ashaka) da kuma BUA.
Binciken Aminiya ya gano cewa farashin siminti ya tashi daga Naira 2,500 zuwa Naira 3,600 a watan Nuwamban bara.
Wani dillalin siminti a Okera a Jihar Legas, Adeleke Oluwafemi, ya ce ana sayar da buhun simintin Dangote a kan Naira 3,400 a kamfani, yayin da su kuma sukan sayar da shi a kan Naira 3,600 a Janairu zuwa Afrilun bana.
Farashin ya tashi lokaci daya, inda a yanzu kamfani ke sayar da shi a kan Naira 4,000 yayin da masu sayarwa suke sayar da shi tsakanin Naira 4,200 zuwa Naira 4,300.
Oluwafemi ya ce ana sayar da Simintin BUA a kan Naira 3,600 a farkon bana, amma yanzu ana sayar da kowane buhu a kan Naira 4,100.
A Babban Birnin Tarayya, binciken da Aminiya ta gudanar a makon jiya ya gano cewa ana sayar da buhun simintin Dangote tsakanin Naira 3,800 zuwa Naira 3,900, ya danganata da wuri.
Bincike a kasuwannin Bwari da Birnin Abuja da Kwali da Kuje da Gwagwalada ya nuna cewa simintin BUA ya dan yi sama, inda ake sayar da shi a tsakanin Naira 3,900 zuwa Naira 4,000.
Ana sayar da simintin Ashaka tsakanin Naira 3,800 zuwa Naira 3,900.
Daya daga cikin dillalan simintin da ya zanta da wakilinmu, ya ce babu tabbacin farashin ba zai kara hauhawa ba a yanzu, muddin masu ruwa-da-tsaki ba su dauki matakin gaggawa ba.
Daga Kano kuwa, ana sayar da simintin Dangote a kan Naira 4,500, BUA Naira 4,700, sai kuma Ashaka Naira 4,450.
Wadansu ’yan kasuwa da suka zanta da Aminiya sun ce an samu karancin simintin a ’yan kwanakin nan.
Sun yi zargin cewa akwai wani shiri na kara farashin simintin don haka ne manyan dillalan suke boye shi.
A Maiduguri fadar Jihar Borno ana sayar da Dangote a kan Naira 4,500 da Ashaka Naira 4,100. Kamfanin BUA, wanda tun kusan mako biyun da suka shige bai kai simintin ba, an sayar da shi a kan Naira 3,500.
— Majalisar Dattijai na son a kara ba da lasisin siminti
Ganin yadda tsadar simintin ta sa jama’a da dama a cikin kunci, Majalisar Dattijai a watan Afrilu ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta samar da karin tallafi ga masana’antun domin a samu sababbin masu shiga harkar siminti don a habaka samar da shi, wanda hakan zai sa farashinsa ya karye.
Majalisar ta ce ta lura cewa hauhawar farashin siminti yana kawo cikas ga gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa da ake bukata domin bunkasa ci gaban kasa.
A watan jiya ne hamshakin dan kasuwar nan na Katsina, Akhaji Dahiru Barau Mangal, ya kulla yarjejeniya da wani kamfanin a kasar China ta Dala miliyan 600, domin kafa kamfanin yin siminti a garin Moba a Jihar Kogi.
Masu kamfanonin siminti sun samu riba mai yawa
Kamfanoni uku, Dangote da BUA da Ashaka sun bayar da rahoton samun ribar Naira biliyan 469 a wata tara da suka gabata.
Kamfanin Siminti na Dangote shi ne kan gaba, inda ya samu ribar Naira biliyan 331.6, sai BUA, Naira biliyan 74.1 shi kuma Ashaka ya samu ribar Naira biliyan 63.6.
Shugaban Rukunin Kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabi’u, a wata tattaunawa da ’yan jarida a farkon shekarar nan ya dora alhakin tashin farashin siminti a kasar nan “A kan yawan bukatar simintin da kuma karancinsa.”
Ya ce, “Najeriya tana da sama da mutum miliyan 200. Idan aka yi la’akari da yadda ake samar da siminti, a bara mun kasance muna samar da kasa da tan miliyan 30.
“Don haka, a zahiri ba mu samar da abin da ya kamata lura da sauran kasashen Afirka, baya ga watakila Jamhuriyar Nijar. Don haka, hakan na nufin ba mu da isasshen kayan aiki.”
A bangaren Kamfanin Siminti na Dangote a kwanakin baya ya ce duk da cewa kamfanin yana da ikon sarrafa tsofaffin masana’antu, amma ba zai iya yin tasiri a farashin kayayyakin idan ya zo kasuwa ba.
Babban Daraktan Kamfanin Dangote, Debakumar Edwin, ya ce kamfanin ya dakatar da fitar da kayayyakinsa zuwa kasashen waje domin biyan bukatun cikin gida.
Haka kuma, ya ce sun sake farfado da kamfaninsu da ke Gboko wanda yake da karfin yin tan miliyan 4.5 a da aka rufe shekara hudu da suka gabata.
An kuma yin hakan ne don ganin farashin simintin ya fadi a kasar nan.
Daga: Sunday M Ogwu, Hussaini Yahaya (Abuja), Ibrahim Kegbegbe (Legas), Clement Oloyede (Kano) & Musbau Bashir (Borno).