✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siffofin “Windows 10” da alakarta da “Windows 7” da “Windows 8” (3)

Wannan yanki ne na karshe a wata tattaunawa da gidan Rediyon BBC ya yi da ni kan wannan manhaj ta Windows,. Don haka nag a…

Wannan yanki ne na karshe a wata tattaunawa da gidan Rediyon BBC ya yi da ni kan wannan manhaj ta Windows,. Don haka nag a ya kamata a zubo wa masu karatu, musamma ma wadanda ke aiko eda tambayoyin neman karin bayani a kan massarafa d amanahajar Kwamfuta.

Ke nan, dabara ce da kamfanin ya yi amfani da ita don a ci gaba da tafiya da shi…
…Dabara ce don a ci gaba da tafiya da shi, saboda ya kwato kwastomominsa da kamfanin Apple da Samsung da sauran kamfanonin kera wayar salula suka kwace masa.  Domin shugaban kamfanin Microsoft, wato Satya Nadella, ya tabbatar da cewa babbar manufar bullo da “Windows 10” ita ce, game dukkan masu mu’amala da na’urorin sadarwa gaba daya.  Ya ce ana sa ran mutum biliyan daya za su yi amfani da wannan babbar manhaja ta “Windows 10” a duniya.  
To idan muka duba ko muka yi la’akari da dabi’u ko siffofin “Windows 10” sai mu ga cewa lallai akwai alamar haka na iya faruwa.  Domin akwai da yawa cikin wadanda suka saba sukan tsarin kasuwanci na kamfanin Microsoft cikin sharhinsu na hanyoyi da na’urorin sadarwar zamani, a halin yanzu da bayyanar babbar manhajar “Windows 10” duk sharhinsu ya raja’a ne wajen yabon wannan sabuwar babbar manhaja.  Abin da kuma ke nuna lallai kamfanin Microsoft ya kama hanya ke nan.
Bayan duk wadannan abubuwa masu kayatarwa da ka bayyana na wannan sabuwar manhaja ta “Windows 10,” sai ga shi kuma kamfanin ya bayyana cewa zai bayar da wannan babbar manhaja ne kyauta.  Me hakan yake nufi?
daya daga cikin abubuwan da ke bai wa mutane mamaki ke nan.  Na nuna mana cewa, da dama cikin kamfanonin (da Microsoft ya saba mu’amalar kasuwanci da su) sun juya masa baya.  Kuma idan ba mu mance ba, lokacin da kamfanin ya fitar da babbar manhajar “Windows bista,” kamfanin HP bai nuna sha’awarsa wajen amfani da wannan babbar manhaja ba,  wanda kuma kowa ya san kamfanin HP babban kamfani ne.  
A lokacin an kiyasta yana da kwamfutoci a kalla sun kai 800 da ke ofishinsa na Amurka kadai, amma ya ki amfani da babbar manhajar “Windows bista,” saboda rashin nagartarta.  Sai ya ci gaba da amfani da tsohuwar manhajar “Windows dP” kawai.  Hakan kuwa ke nuna lallai kamfanin Microsoft ya rasa hatta mafi kusancin kamfanonin da ke kawancen kasuwanci da shi ke nan.
Da Microsoft ya gano haka, sai ya mayar da wannan babbar manhja ta “Windows 10” ta zama kyauta.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, idan kana da kwamfuta wacce ke dauke da “Windows 7,” ko in ce “Windows 7.1,” – wadda ita ce ta gaba-gaba a nau’in “Windows 7.”  Da kuma (masu amfani da) “Windows 8” ko “Windows 8.1,” nan take kyauta za ka iya samun wannan babbar manhaja ta hanyar “Windows Update” (da ke cikin Windows da kake amfani da ita).  Tsarin “Windows Update” cibiya ce da babbar manhajar Windows ke amfani da ita wajen samar wa kwamfuta bayanan karin tagomashi da nagarta, (kai tsaye daga cibiyar manhajoji na kamfanin Microsoft)…
…Ke nan ashe kai ma kyauta za ka samu ke nan…
…Sosai ma.  A halin yanzu kwamfuta ta tana can tana saukar da wannan babbar manhaja kyauta!  Abin da wannan ke nufi shi ne, in dai kana da “Windows 8” ce, kai tsaye kwamfutarka za ta saukar da wannan babbar manhaja (nauyinsa wajen 2.8GB ne. Duk da cewa kamfanin ya tallata wa masu bukata ne ta hanyar cibiyar Windows Update, makonni uku kafin ranar kaddamarwa.  Duk wanda ya karbi tayin, yana cikin wadanda za su fara samun damar saukarwa), amma duk da haka, akwai alamar nan gaba tilascin kamfanin na iya sa dole sai ka saukar da “Windows 10.”
Ga wanda ba shi da “Windows 7” ko “Windows 8” ko Windows na baya, shi ma kyauta zai samu?
A a, ba zai samu kyauta ba, gaskiya.  Saboda “kyauta” da aka ce, wannan kalmar ta shahara ne saboda kamfanin Microsoft bai taba yin wani abu makamancin haka ba a baya.  Idan kana amfani da babbar manhajar kamfanin Microsoft, kowace iri ce, da zarar ya sake fitar da wata sabuwar babbar manhaja, dole ne ka je kasuwa ko shagon da ake sayar da manhajojin kwamfuta (Computer Shop) ka sayi faifan CD ko DbD mai dauke da manhajar, ko kuma ka saya daga shafinsa na yanar gizo, ta amfani da katinka na ATM, (ko kuma ka sayi sabuwar kwamfuta mai dauke da sabuwar babbar manhajar, misali.   Amma batun ka saukar da babbar manhajar ta kwamfutarka (kyauta), ba a taba samun haka ba daga kamfanin Microsoft sai wannan lokaci.
Kuma kamar yadda na gaya mana a farko, babbar manufar (yin hakan) dai don a bai wa mutane hakuri ne cikin dabara, a kuma jawo hankalinsu don nuna musu cewa a halin yanzu tafiya ta gyaru kuma in sha Allahu nan gaba abubuwa ba za su ci gaba da kasancewa kamar yadda suka kasance a baya ba.
Wannan tsari na samar da wannan babbar manhaja kyauta ga wadanda suke da manhajar a baya, wani tasiri zai yi ga abubuwan da suke faruwa na jama’a da dama da suke kokarin samar da wannan manhaja ta kasuwar bayan fage?
Eh to, wannan shi ake kira “Piracy,” kuma a duniyar sadarwa babu kamfanin kera manhajar kwamfuta da ake samun manhajojinsa na kasuwanci masu dan karen tsada, ta hanyar kasuwar bayan fage irin kamfanin Microsoft.  Wanda wannan shi ne dalilin da yasa kamfanin ya saduda gaba daya.  Domin tun yana fada da masu irin wannan dabi’a a bayyane, har abin ya buwaye shi.  Don ba fada ba ne da zai iya cin galabarsa.  Domin akwai masana harkar kwamfuta masu mummunar nufi (kamar ‘yan Dandatsa, wato “Hackers,” misali), masu kwarewa wajen iya waske duk wata kariya da kamfanin yake sanyawa a cikin babbar manhajar.  Kuma wadannan mutane sun san inda kowace matsala ko rauni take a jikin babbar manhajar.  Don haka suna iya jujjuya wadannan manhajoji yadda suke so.
Yanzu haka da nake magana, ka ga dai “Windows 10” yau ake kaddamar da ita, amma makonni sama da uku da suka gabata (kafin wannan rana), akwai shafukan da idan ka je a Intanet za ka iya samun babbar manhajar, ka saukar da ita, kuma irin wadda ke kamfanin Microsoft din.  Duk me ya jawo haka?  Saboda akwai wadanda suke da karfin kwarewa na ilimi (amma masu mummunar manufa), wanda kuma za su iya saukar da manhajar ta hanyoyin da suka sani na bayan fage – wanda ba abu ne da bayaninsa zai iya yiwuwa a halin yanzu ba – su sarrafa su kuma canza wa manhajar dabi’a.  Idan ma kamfanin Microsoft ya sanya wata ka’ida da ta shafi shigar da wasu kalmomi ko lambobi ne (a yayin da aka zo loda manhajar a kwamfuta) kafin a iya amfani da ita, su za su iya waske wannan ka’ida, saboda suna da kudurar yin hakan.
Bayyanar “Windows 10” tabbas zai iya rage hanyoyin da ake bi wajen samar da manhajojin kamfanin Microsoft a bayan fage, domin abin da yake tabbace a yanzu shi ne, duk wanda ya mallaki “Windows 10,” to ya mallaki babbar manhajar Windows ta karshe.  Kamfanin Microsoft ba zai kara fitar da wani nau’in babbar manhaja ba, wannan dai ce za a ci gaba da kayatar da ita tare da inganta ta.  Kuma idan kana da babbar manhajar “Windows 10” a wayar salularka, iri daya ce da wadda take dauke a kan kwamfutarka.  Kuma kamar yadda nayi bayanin dabi’u da siffofin “Windows 10” a baya, kari a kan haka, idan kana da “Windows 10” a kan kwamfutarka a halin yanzu, ka zo da wayar salularka, akwai tsarin da zai iya ba ka damar kulla alaka a tsakaninsu, har ka rika ganin shafin da kake ciki a kan kwamfutarka.
Wannan ke nuna cewa dabi’un wannan sabuwar babbar manhaja sun sha bamban da na wadanda kamfanin ya fitar a baya.  To, wannan kuma ke tabbatar da cewa, ko za a samu wasu a bayan fage, to ba lalai bane su zama daidai da irin wanda kamfanin ya bayar.  Me yasa?  Saboda akwai abin da ake kira: “Seamless interaction,” wato: “Tsarin mu’amala tsakanin hanyoyi da na’urorin sadarwa ba tare da matsala ba,” wanda ke samuwa tsakanin kwamfuta da wayar salula, da sauran na’urorin sarrafa bayanai.  
A halin yanzu kamfanin Microsoft ya gina wannan tsari a cikin “Windows 10.”  Don haka, idan mutum ya sayi “Windows 10” a kasuwar bayan fage, muddin za ka jona kwamfutarka da Intanet, to dole ne za ta rika samun musayar bayanai tsakaninta da shafin Microsoft.  A baya ne sai ka ga dama haka ta yiwu, amma a wannan zamani ana samun wannan musayar bayanai ta hanyoyin da mai kwamfuta ma bai san da su ba.
 A haka za a iya gano cewa “Windows 10” dinsa ba ingantacciya ba ce, kuma sanadiyyar haka ana iya dakile dukkan hanyoyi ko siffofinta masu nagarta, ba zai iya mu’amala da su ba balle ya kwashi dimbin fa’idar da ke tattare da su.
To, Baban Sadik muna godiya matuka.
To, Alhamdulillah!