Daya daga cikin limamai na din-din-din a Masallacin Harami da ke Makkah, Sheikh Saud Ash Shuraim ya yi murabus daga aikin limancin masallaci.
Cikin wata sanarwa da shafin Haramain Sharifain ya fitar a shafinsa na sada zumunta, ya ce Shuraim ya yi murabus din ne bayan shafe shekaru 32 yana gudanar da aikin limanci.
Imam Shuraim ya ce wasu dalilai na kashin kai ne suka sanya shi ajiye makamin jagorancin sallar.
Sai dai bayanai na cewa zai iya komawa ya ci gaba da jagoracin sallar tarawihi a matsayin bakon limami, wanda za a sanar da dalilan haka nan da makonni masu zuwa.
Alkaluman tarihi sun nuna an haifi Sheikh Sa’ud Ibn Ibrahim Ibn Muhammad Al-Shuraim a ranar 19 Janairu 1964 a birnin Riyadh na Saudiyya.
Shiekh Shuraim ya yi karatun firamare a Areen Elementary School.
Sannan ya yi karatun sakandire a Modern School for Secondary Education.
Sannan ya yi karatun gaba da sikandare a makaranatar Al-Yarmouk North High School wacce ya kammala a shekarar 1983.
Ya kuma halarci jami’ar Imam Muhammad Bin Saud, indq ya kammala a shekarar 1988.
Ya ci gaba da karatu har ya kai ga matakin samun shaidar digirin digirgir.