Takaddamar shugabanci da ta dabaibaye Masallacin Darul Hadith na Marigayi Dokta Ahmad Ibrahim Bamba da ke Unguwar Tudun Yola a Kano, ta kai munzalin dakatar da gudanar da sallar Juma’a a cikinsa.
An dai nemi a bai wa hammata iska yayin da sabon limamin masallacin ke shirin hawa mimbari domin fara gabatar da hudubar Juma’a, inda wasu fusatattun masu ruwa da tsaki suka dakatar da shi ta hanyar riko tufafin da ke sanye a jikinsa.
- Za a iya samun bullar Covid-19 fiye da yadda aka fuskanta a baya —NCDC
- An haramta wa tsohon Shugaban Mauritania fita ketare
Wannan lamari dai ya sanya aka rufe masallacin nan take kuma jami’an tsaro suka yi masa kawanya.
Tuni bangarorin biyu da ke takaddama a kan masallacin suka shigar da korafinsu a gaban rundunar ’yan sandan Jihar Kano, domin ta shiga tsakani a samu masalaha.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mazauna Unguwar Tudun Yola da ta kasance matsugunar masallacin na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata tarzoma ba.
Sai dai da Aminiya ta kara bin diddigin lamarin, ta gano cewa rikicin da aka yi ba shi da nasaba da limanci, hasalima an yi sallar Juma’a a Masallacin.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce “a ranar Alhamis Sarki [Aminu Ado Bayero] ya kiramu Fada za a yi nadin limancin.
“To mun je Fadar, sai a ka samu akasi, Sarkin Katsina da na Bauchi sun zo a lokacin, sai Sarki zai je ya taro su, saboda haka sai ya turamu ofishin Waziri ya yi nadi.
“Sai dai kash! Shi kuma waziri bai shigo ba, sai ranar Litinin zai zo.
“To mutanen unguwa ba su ji dadi abin ba, saboda daman kowa a wuya yake.
“Kuma daman gudun samun hargitsi ne ya sa ake so hukuma ta shiga cikin lamarin, saboda ’yan unguwa abin ya ishesu, sun gaji da abinda ’ya’yan Dokta [Marigayi Ahmad Bamba] su ke yi na kin barin magajinsa ya hau kujerar babansu.
“To kawai jiya ina gida sai aka kirani aka ce ana hargitsi, to ni kuma jiya [Juma’a] wani ikon Allah ban je masallacin ba.
Ba a hana sabon limami jan sallah ba
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Amma maganar cewa sabon limamin aka hana sallah ba haka ba ne gaskiya.
“Shi ba sallah ya je ba, ya je daurin auren daya daga cikin ladanan masallacin ne wanda aka daura a jiya.
“Labaran da ake yadawa cewa sabon liman ko kuma magajin malam ya zo sallah an kaure da rikici ba haka ba ne ba.
“Maganar gaskiya ita ce; shi magajin da malam ya bari da wasiyyar cewa shi zai jagoranci al’amuran yau da kullum na masallaci da kuma limancin a yau ko kuma shiga wani al’amarin masallaci ba shi da alaka da maganar limanci.
“Hasalima daurin auren daya daga cikin ladanan masallacin wanda shi ya dauke shi aiki da hannunsa a lokacin da yana limanci kuma Darekta a masallacin.
“Saboda haka daurin aurensa ya je ya ga an hana shi limamin da ya kamata ya ja sallar Juma’ar ta yau.
“Kuma dai kullum dama shi limamin ne ya saba jagorancin sallar Juma’ar tun bayan rasuwar Malam kuma a yau din kamar yadda yake a tsari cewa shi ne zai yi sallah yau amma wasu yan kama karya da suke da’awar jagorancin masallaci suka hana shi.
“Saboda haka wannan lamari ya fusata al’ummar Unguwar har suka sanya shi wannan limamin na su a gaba don ya jagoranci sallah.
“Kuma AlhamdulilLah an yi sallar Jumu’ar yau 6 ga watan Janairun 2023.”