Shugabannin Tsaron Najeriya na ganawar sirri da Majalisar Tarayya inda za su yi bayani game da halin da ake ciki da hanyoyin magance matsalar tsaro da ke addabar kasar.
Kafin faga ganawar ta sirri, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana wa Shugabannin Tsaron cewa ba su yi abin da ake bukata ma domin magance matsalar tsaron da ke Najeriya tarnaki.
“Ina tabbatar muku cewa Majalisa ta dauki duk abubuwan da kuke fuskanta da matukar muhimmaci.
“Kusan kullum sai Majalisar Dattawa ta tattauna wani abun da ya danganci tsaro, kuma an kwashe shekaru ana hakan,” kamar yadda ya ce.
Sai dai ya danganta matsalolin da hukumomin tsaron ke samu da rashin isassun kayan aiki, don haka ya bukaci su yi wa Majalisar bayani domin ganin yadda za a kawo karshen matsalar.
Ya kuma ba sa tabbacin cewa Majalisar za ta ba su duk taimako da goyon bayan da suke bukata domin samun nasara wari kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Najeriya.
Da farko Majalisar ta nemi zama da Shugabannin Tsaron ne ranar Talata, amma aka dage shi zuwa Alhamis, saboda za su halarci zaman Majalisar Tsaron Kasa a ranar Talata.
Mahalarta zaman sun hada da Shugabannin Rundunonin Soji, Shugaban Hukumar Leken Asiri, Shugaban ’Yan Sanda, Ministan Tsaro, da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro.