✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin Najeriya da Masu Jefa Ƙuri’a Na Yaudarar Kansu —Ibrahim Yusuf

“Wannan yanayi na ƙunci da tsadar rayuwa, mu muka jawo wa kanmu.

Shugaban haɗakar ƙungiyoyin farar hula na Jihar Gombe (ANGO), Kwamared Ibrahim Yusuf, wanda aka fi sani da “3000”, ya ce shugabannin Nijeriya da ‘yan ƙasar masu jefa ƙuri’a suna yaudarar kansu a tsarin jagorancin da ake gudanarwa a halin yanzu.

Kwamared Ibrahim Yusuf ya bayyana cewa “shugabannin ba sa damuwa da halin da talakawa suke ciki sannan babu wanda zai iya fitowa ya gaya musu cewa ana bukatar gyara, saboda suna ganin cewa kudin da suka kashe ne ya ba su nasara a zaɓe.

“Saboda haka, ba su damu da korafe-korafen jama’a ba, saboda suna tunanin cewa ba a isa a yi musu magana ba.”

Yusuf ya bayyana hakan ne a wata hira da wakilinmu, inda ya ce tun farko shugabannin sun hau karagar mulki ne da nufin azurta kansu da kudin jama’a.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa suka kashe kuɗinsu domin samun nasarar zaɓe, kuma hakan yana nuni da cewa ba sa damuwa da koke-koken da al’umma ke yi.”

Ya kuma ƙara da cewa, “’yan kaɗan daga cikin jama’a waɗanda ba su karɓi kuɗin ’yan siyasa ba, ba su da wata hanyar da za su gabatar da buƙatunsu ga waɗannan shugabannin, ballantana a saurare su domin a yi gyara.

Yusuf ya ƙara da cewa “wannan yanayi na ƙunci da tsadar rayuwa, mu muka jawo wa kanmu ta hanyar karɓar kuɗin shugabanni da sayar da ’yancinmu.

“Saboda haka, babu makawa sai mun haƙura har zuwa ƙarshen wannan lamari, domin babu wani shugaba da ke tausaya wa al’umma kan halin da suke ciki.

Ya ƙara da cewa, “idan shugabannin suna sauraron wani, to iyayen gidansu ne waɗanda suka ɗaure musu gindi a siyasa, waɗanda su kansu ba damuwa suke da al’umma ba.”