Matar Gwamnan Jihar Kaduna, Ummi El-Rufa’i ta yi kira ga shugabannin addini da na gargajiya da su daina kare masu fyade a garuruwan da suke.
Ummi ta yi kiran ne a lokacin da ta ziyarci shugabannin addini da gargajiya don fadakar da su kan illar fyade da cin zarafin mata a garin Turunku na Karamar Hukumar Igabi, a ranar Jumu’a.
“Dole a daina kare masu cin zarafi da yi wa mata fyade”, inji ta
Ta kuma ce, matsalar fyaden yara kanana sai kara yawaita yake yi a jihar, lamarin da ta danganta da bayar da kariyar da masu aikatawa suke samu daga shugabannin al’umma.
“Mun zo ne domin ci gaba da fadakarwa a kan fyade, sannan kuma mu hadu da shugabannin al’mma, na gargajiya da na addini da sauran masu fadi a ji don su taimaka wajen yaki da abun.
“Muna samun labarin wani lokacin shugabannin al’umma ke ba su kariya. Mun zo ne mu gaya muku cewar ku daina, saboda idan har aka ci gaba da yafe musu saboda makwataka ko ‘yanuwantaka da ke tsakani ko kuma kare yarinyar daga tsangwama ko a ki auren ta, to masu fyaden ba za su daina ba. Za su ci gaba da lalata yaran da zaran an yafe musu.” inji El-Rufai.
Ta kuma yi kira ga al’umma da su daina tsangwamar wadanda aka yi wa fyade saboda ba laifinsu ba ne.
A nashi jawabin, Mai Garin Turuku Sabuwa, Alhaji Ibrahim Usman, ya gode wa matar gwamnan kan zabar garinsa da ta yi a matsayin wuri na farko da aka yi fadakarwa a kan kawo karshen fyade.