✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugabancin WTO: Buhari ya yaba da goyon bayan Amurka ga Okonjo-Iweala

Goyon bayan zai sa ’yar Najeriya ta zama Shugabar WTO ta farko mace kuma daga Afirka

Shugaba Buhari ya yi maraba da goyon bayan da sabuwar Gwamnatin Amurka ta bayar da zai kai ’yar Najeriya ga zama Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) mace ta farko kuma daga nahiyar Afirka.

Sanarwar da ya fitar ranar Asabar ta ce janywar da Gwamnatin Shugaba Joe Biden ta yi daga kalubalantar takarar tsohuwar Ministar Kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala na zama sabuwar Darakta-Janar ta WTO ya faranta ran daukacin Afirka.

Buhari ya ce, “Najeriya da ma daukacin Nahiar Afirka na murna da matakin na sabuwar gwamnatin Amurka da zai kawo kyakkyawan sauyi a huldar da ke tsakanin kasashen Afirka da sabuwar Gwamntin Biden.

“Yanzu Amurka na tare da Najeriya da ma Afirka ta hanyar goyon bayan ’yar kasarmu, Okonjo-Iweala ta jagoranci WTO.

“Za mu yi aiki tare da sabuwar gwamnatin Amurka ta wannan fuska da sauran al’amura da ke tsakaninmu, musamman habaka tattalin arziki da wuri, yaki da ta’addanci da kuma bunkasa cigaba,” inji sanarwar.