Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta amince da rabon mukamai na shugabancin majalisa ta goma.
APC ta ce ta amince da Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa daga shiyyar Kudu maso Kudu.
- An kama dan Najeriya yana safarar Hodar Iblis a Saudiyya
- ISWAP ta kashe manoma 3, ta sace 11 a Borno
Haka zalika, Sanata Barau Jibrin zai kasance Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan daga Arewa maso Yamma.
Wata sanarwa da jam’iyyar mai mulki ta fitar, ta ambato kwamitin gudanarwa na APC yana cewa matakin ya zo ne bayan rahotannin tuntuba da tarukan da jam’iyyar ta yi da Zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar ta ce haka kuma wannan na zuwa ne bayan tuntubar shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki game da rabon mukamai zuwa shiyyoyi daban-daban na kasar game da jagorancin majalisa ta goma
A Majalisar Wakilai kuma, APC ta ce tana goyon bayan Abbas Tajuddeen a matsayin shugaban majalisar ta wakilai daga Arewa maso Yamma.
Sai Ben Kalu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai daga Kudu maso Gabas.
Sanarwar ta ce Kwamitin Gudanarwar APC na Kasa ya lura cikin mutuntawa da sakamakon taruka tsakanin zababben shugaban kasa da shugabancin kwamitin.
Wannan mataki ya tabbatar da rade-radin da aka dade ana yi cewa APC ta bai wa Sanata Godswill Akpabio matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Abbas Tajuddeen matsayin Shugaban Majalisar Wakilai da za a bude a nan gaba.
Da wuya a iya sani zuwa yanzu, ko wannan mataki na jam’iyyar mai mulki, zai kawo karshen dambarwa da kai ruwa-ranar da ake yi game da neman shugabancin majalisa ta goma.
Sai a watan Yuni ne za a kaddamar da sabuwar majalisar, wadda za ta yi aiki kafada da kafada da Zababben Shugaban Kasar, Bola Ahmed Tinubu.
A baya, zaben shugabannin majalisun tarayya ya saba zuwa da zafi, da kuma nuna bijirewa ga shugabancin jam’iyya mai mulki da kuma bangaren zartarwa.
Ko a majalisa ta takwas a shekara ta 2015, ’yan Majalisar Dattawa sun bijire wa umarnin jam’iyyar APC mai mulki, inda suka zabi Sanata Abubakar Bukola Saraki, matsayin shugabansu a kan dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Ahmad Lawan.
Yayin da Majalisar Wakilai ta zabi Yakubu Dogara, maimakon Femi Gbajabiamila, dan takarar da jam’iyyar ta goyi baya a lokacin.
Lamarin dai ya janyo zaman doya da manja a wa’adin farko na jam’iyyar APC, bayan ta kwace mulki daga hannun PDP.