Yayin da shirye-shirye suka kankama na gudanar da Babban Taron Jam’iyyar APC na kasa ranar Asabar mai zuwa, daya daga cikin masu neman shugabancin jam’iyyar na kasa, Dokta Sani Abdullahi Shinkafi ya janye daga takararsa.
Dokta Shinkafi, wanda tsohon Sakataren Jam’iyyar APGA na Kasa ne, kafin ficewarsa zuwa Jam’iyyar APC tare da Gwamna Matawalle, ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Gusau ranar Talatar da ta gabata.
- Matashi ya hallaka matar aure da tabarya bayan ya sace wayoyinta a Kano
- Mun kama kilogiram 374.47 na Tabar Wiwi cikin wata 2 a Kano – NDLEA
A cewarsa, janyewar tasa ta biyo bayan tabbatar da kujerar ga yankin Arewa ta Tsakiya da aka cin ma matsaya a kai, yankin da Sanata Abdullahi Adamu ya fito, inda kuma Majalisar Zartarwar Jam’iyyar APC ta Kasa ta yi kuma Sanata Adamun ke neman wannan kujera.
“Ina so in jaddada cewa ina mutunta shawarar da babbar jam’iyyarmu ta yanke na cewa shugaban Jam’iyyar APC a matakin kasa zai fito daga yankin Arewa ta Tsakiya kuma a kan haka na janye takarata,” inji Shinkafi.
Idan za a iya tunawa, rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa na nuni da cewa, Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayan takarar Sanata Adamu ne, kamar yadda rahotanni da dama suka tabbatar.
Dokta Shinkafi ya ci gaba da nuna cewa ficewarsa daga takarar ta biyo bayan girmamawa da ya ke yi ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
“Ina so in shaida muku cewa, a yau na yanke shawarar janyewa daga takara a matsayin mutum mai mutunta martabar jam’iyya da shugabannin jam’iyyar tare da mutunta Shugaban Kasa,” inji shi.
Ya ce, “Shugaba Buhari ne jagoran jam’iyyar kuma ya dauki matsayin. Na sha fada muku cewa zan tsaya takara idan har aka sanya shiyyar Arewa maso Yamma. Ba na so in yi adawa da abin da shugabana ya faxa.”
Ya yaba wa duk wadanda suka mara masa baya a lokacin gwagwarmayar tsayawa takarar Shugaban Kasa, musamman Gwamna Bello Matawalle, Shugaban Riko na Kasa, Mai Mala Buni, Gwamna Zulum da dai sauransu. Ya kuma yi alkawarin ci gaba da bai wa shugabannin jam’iyyar goyon baya a matakin jiha da kasa baki daya, domin samun damar kammala babban taron kasa mai zuwa cikin nasara da zaman lafiya.