✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabancin EFCC: Kotu ta kori karar neman tsige Olukoyede

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya yi watsi da karar ne bisa hujjar cewa mai karar ba shi da hurumin shigar da karar.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori karar da ke neman a kori Mista Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya yi watsi da karar ne bisa hujjar cewa mai karar ba shi da hurumin shigar da karar.

Wani lauya mazaunin Abuja, Victor Opatola, ne ya kai karar shugaban kasa Bola Tinubu kan nadin Olukoyede a matsayin shugaban EFCC.

Opatola ya kalubalanci sahihancin nadin bisa hujjar cewa Olukoyede bai cika shekarun aikin da doka ta bukata domin rike ofishin shugaban hukumar ta EFC ba.

Ya sanya sunayen Shugaban Najeriya, Majalisar Dokoki ta kasa, Atoni-Janar na Tarayya (AGF) da Olukoyede a matsayin wadanda ake kara.

Sai dai wadanda ake kara sun roki kotun da ta yi watsi da karar saboda rashin cancantar shi.

Olukoyede, wanda Olumide Fusika, SAN, ya wakilce shi a ranar da aka dage sauraron karar, ya kalubalanci hurumin wanda ya shigar da karar da ya shigar da karar a matakin farko.

Bayan haka, Olukoyede ya yi ikirarin cewa ya cancanci zama Shugaban EFCC, bayan ya rike mukamin sakataren hukumar, wanda ke matakin albashi na 17, wanda ya zarce matsayin mataimakin kwamishinan ’yan sanda da ke mataki na 14.

Don haka ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar.