Shugaban Yemen ya mika ikon da yake da shi ga wani Kwamitin Shugaban Kasa na musamman tare da korar mataimakinsa Ali Mohsen al-Ahmar daga mukaminsa.
Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi ya ce daga yanzu kwamitin ne zai ci gaba da tafiyar da sha’anin siyasa, da sojoji, da kuma tsaron kasar Yemen.
- Za a yi gwanjon rigar Maradona kan fam miliyan 4
- Sukar gwamnati: Yanzu aka fara – Sheikh Nuru Khalid
BBC ya ruwaito a jawabin da ya yi ta talbijin, Shugaba Hadi ya ce sabuwar gwamnati za ta kawo karshen zubar da jinin da ake yi a ƙasar.
Kwamitin mai mutum bakwai zai yi aiki karkashin jagorancin tsohon ministan cikin gida Rashad Al-Alimi.
Tuni Saudiyya ta yi maraba da matakin, tana mai neman sabuwar gwamnati ta tattauna da ’yan tawayen Houthi saboda samun dawwamammen zaman lafiya da kawo karshen yakin basasar shekara bakwai.
Bayan shafe tsawon shekaru ana gwabza yaki a Yemen ’yan tawayen Houthi sun cimma yarjejeniyar tsagaita buda wuta da kawancen sojin da kasar Saudiyya ke jagoranta.
Yarjejeniyar da aka cimma karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya za ta shafe tsawon watanni biyu ne a kasar da yaki ya daidaita, kana kuma tuni ta soma aiki ranar Asabar, daya ga watan Ramadana.
Bangarorin biyu da suka aminta da tsagaita buda wuta, sun kuma yi na’am da zirga-zirgar jirage daga wasu yankuna zuwa babban birnin kasar Yamen Sana’a, baya ga bude mashigar ruwa ta Hodeida da ke yammacin kasar ga tankokin dakon danyen mai, a cewar manzo na musamman na MDD da ya shiga tsakani, Hans Grundberg.