✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban ‘Yan Tumatir na Kasuwar Mil 12 ya rasu

Allah Ya yi wa Shugaban Sashen ’Yan Tumatir na Kasuwar Mil 12 da ke Legas Alhaji Yahuza Bagobiri rasuwa sakamakon hadarin da ya yi a…

Allah Ya yi wa Shugaban Sashen ’Yan Tumatir na Kasuwar Mil 12 da ke Legas Alhaji Yahuza Bagobiri rasuwa sakamakon hadarin da ya yi a kan babur.

Marigayi ya gamu da ajalinsa ne bayan da wata babbar mota ta ture shi yana kan babur a makon da ya aurar da ’ya’yansa mata su biyar kuma ya yi kara aurar mace a garin Zarewa Da ke jihar Kano. An kwantar da marigayin a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a Jihar Kaduna bayan hadarin inda ya rasu cikin dare  ranar Litinin da ta gabata.