Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya fara wata ziyarar aiki ta kwana biyu a Najeriya ranar Talata.
Babban mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a Abuja ranar Talata.
- El-Rufa’i ya ba ma’aikatan Kaduna kwana 12 su yi rigakafin COVID-19
- Masu zanga-zangar #EndSARS sun fantsama a titunan Abuja
A cewar sanarwar, Shugaba Erdogan, wanda ya sami rakiyar mai dakinsa, Emine, ya zo Najeriya ne daga kasar Angola, kuma zai wuce Togo a wata ziyarar karfafa dangantaka da yake yi a wasu kasashen Afirka.
Yayin ziyarar, Shugabannin biyu za su tattauna yarjeniyoyi da dama musamman na tattalin arziki tsakanin kasashensu.
Sanarwar ta ce baya ga tattaunawar, Shugaba Erdogan zai kuma jagoranci kaddamar da Cibiyar Kula da Al’adu ta Kasar Turkiyya a Abuja.
A nata bangaren, Emine Erdogan, za ta sami rakiyar uwargidan Shugaba Buhari, Aisha domin kaddamar da sabon ginin Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Wuse II a Abuja, wacce Hukumar Bayar da Tallafi ta Gwamnatin Turkiyya (TIKA) ta gyara.
Garba Shehu ya ce Najeriya na daukar Turkiyya a matsayin babbar kawa, inda ya ce ziyarar za ta taimaka sosai wajen kara karfafa alakarsu.