Shugaban tsagin jam’iyyar PRP na kasa, Farfesa Sule Bello, ya rasu
Ya rasu ne ranar Lahadi a Zariya, Jihar Kaduna yana da shekara 73 bayan ya yi fama da gajeruwar jinya.
- Kungiyar mata lauyoyi ta tallafawa matan da aka ci wa zarafi a Yobe
- An kama matashi dauke harsasai 340 da ya boye a cikin buhun garin rogo
Wata majiya da ked a kusanci da mamacin ce ta tabbatar wad a Aminiya rasuwar tasa, inda ta ce za a yi jana’izarsa a gidansa da ke kan titin Maiduguri Road a unguwar Hotoro da ke Kano da karfe 4:00 na yammacin Lahadi.
Kafin rasuwarsa, shugaban dai malami ne a sashen Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Kwana daya kafin rasuwar tasa, said a wata kungiyar matasa a Kano ta gayyace shi ya gabatar da makala a bikin cikar Najeriya shekara 61 da samun ’yancin kai, amma sai dai wani ya wakilce shi saboda rashin lafiyar.