Shugaban kungiyar teloli ’yan asalin Arewa, reshen Jihar Edo, mazauna garin Benin, Alhaji Shehu Baba danbatta ya bayyana muhimmancin hadin kai da amfaninsa a kungiyance da cewa lamari ne da ke sa a kai ga cin nasara.
“Hada kai da yin aiki da gaskiya cikin sana’a yana sa komai na jama’a ya zo musu da sauki da amfani a cikin harkokinsu na rayuwa, musamman ma in a kungiyance na. Mu kungiyarmu ta teloli, reshen Jihar Edo, ina jan hankalinmu da hada kanmu a kan gaskiya da cika alkawura da muke daukar wa mutane masu kawo mana aiki. Idan muka yi haka, lallai za mu samu ci gaba da kuma samun yarda daga jama’a.
“Akwai bukatar mu dauki wannan sana’a tamu da muhimmanci domin cigabanmu da samun rufin asirin da ke cikinta. Muna da muhimmin matsayi na taimakon al’ummar duniya saboda yadda suke amfani da basira da hikimarmu wajen tsara kowane dinki, saboda haka ina kira ga kowane tela, ba wai a nan jihar kadai ba, ko’ina yake da ya kula da kayan jama’a ya rike gaskiya tare da bayar da hadin kai domin ciyar da sana’ar gaba”. Inji shi.
Alhaji Shehu ya koka a kan rashin samun aikin dinki da ’ya’yan kungiyarsa suke fama da shi a yanzu, saboda kasancewar kasa tana fama da talauci na rashin kudi a yanzu.
Shugaban teloli ya yi kira a kan hadin kai
Shugaban kungiyar teloli ’yan asalin Arewa, reshen Jihar Edo, mazauna garin Benin, Alhaji Shehu Baba danbatta ya bayyana muhimmancin hadin kai da amfaninsa a kungiyance…