Shugaban Kasar Sri Lanka, Gotabaya Rajapaksa, ya mika takardar aikinsa a hukumance jim kadan da saukarsa a kasar Singapore bayan ya gudu ya bar kasarsa.
Matakin na zuwa ne bayan ’yan kasar sun shafe tsawon kwanaki suna zanga-zangar neman Shugaban ya sauka daga mukaminsa kan rikice-rikicen tattalin arziki mafi muni da take fama da shi a tarihinta.
- Mun lalata gonakin Tabar Wiwi masu fadin hekta 2 a Imo – NDLEA
- Hana sayen kuri’u ba aikinmu ba ne —INEC
Ofishin Kakakin Majalisar Kasar ne ya tabbatar da karbar wasikar a ranar Alhamis, inda ya ce Rajapaksa ya tura takardar ce ta email, ’yan sa’o’i bayan ya sauka a kasar ta Singapore.
A ranar Laraba ce dai tsohon Shugaban ya gudu zuwa kasar Maldives, inda daga can ya wuce Singapore din.
Sai dai mai magana da yawun kakakin, Indunil Yapa, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa za su duba ingancin takardar don tabbatar da gaskiyarta, kuma zuwa ranar Juma’a a ke sa ran sanarwarsa a hukumance.
Rajapaksa shi ne ya zama Shugaban Sri Lanka na farko da ya ajiye mukaminsa tun da kasar ta koma tsarin shugaban kasa mai cikakken iko a shekarar 1978.
A bisa Kundin Tsarin Mulkin kasar dai, Firaministan kasar, Ranil Wickremesinghe, wanda shi ma masu zanga-zangar ke neman ya sauka, shi ne zai zama Shugaba na rikon kwarya har zuwa lokacin da majalisa za ta nada magajinsa.