Shugaban kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya rantsar da sabon Firai Minista da kuma sabbin ministoci 18 a ranar juma’a.
Rantsarwar ta biyo bayan cin zaben shugaban wanda majalisar kasar ta gudanar a ranar 20 ga watan Yulin da muke ciki.
- Rasha da Ukraine na kulla yarjejeniyar fitar da hatsi kasuwar duniya
- Takarar Musulmi 2 ce ta sa na ki daukar Tinubu a matsayin mataimaki a 2007 —Atiku
An gudnar da zaben ne bayan tsohon shugaban kasar, Gotabaya Rajapaksa ya ajiye ragamar mulkin kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa an jibge dubban jam’ian tsaro a gaban ofishin Fira Ministan inda aka rantsar da ministocin domin dakile wani abu da ka iya kawo katsalandan.