Shugaba Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministocin da Majalisar Dattawa ta tantance, a ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne, ya sanar da hakan a shafinsa na sada zumunta.
- Da ni ne a kan mulki da Najeriya ba ta shiga tasku ba — Atiku
- Bayan hukuncin CAF an fara kamen ’yan Najeriya a Libya
Idan za a tuna, a ranar 23 ga watan Oktoba ne, Shugaba Tinubu ya sallami ministoci biyar tare da naɗa wasu sabbi guda bakwai.
A ranar 30 ga watan Oktoba, Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabbin ministoci.
Sabbin ministocin sun haɗa Dokta Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan Harkokin Jin-Ƙai da Rage Talauci, Muhammadu Maigari Dingyadi a matsayin Ministan Ƙwadago da Ayyuka, da Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin Ƙaramar Ministar Harkokin Waje.
Sauran sun haɗa da Dokta Jumoke Oduwole a matsayin Ministan Masana’antu, Kasuwanci, da Zuba Jari, Idi Mukhtar Maiha a matsayin Ministan Harkokin Dabbobi, Yusuf Abdullahi Ata a matsayin Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane da kuma Dokta Suwaiba Said Ahmad a matsayin Ƙaramar Ministar Ilimi.