✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban rikon Sri Lanka ya sanya sabuwar dokar ta baci

Shugaban riko na kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya sanya sabuwar dokar ta baci a kan wadda ya sanar a makon jiya

Shugaban riko na kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya sanya sabuwar dokar ta baci a kan wadda ya sanar a makon jiya.

Ranil Wickremesinghe ya ce sabuwar dokar ta bacin na da muhimmanci domin samar da lumana da ci gaban harkoki a fadin kasar da ke fama da durkushewar tattalin arziki da ya yi sanadiyyar yi wa tsohon Shugaba Gotabaya Rajapaksa bore, har ya yi murabus.

Sanya dokar ta bacin “Na da muhimmanci ga tababtar da tsaron al’umma da tabbatar da doka da kuma jigilar muhimman bukatu masu muhimmaci ga rayuwar jama’a,” inji sanarwar da gwamantin rikon kwaryar ta fitar a ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne a yayin da ake sa ran zabar sabon shugaban kasar da zai gaji Rajapaksa a wanna wannan makon.

A ranar Talata za a gabatar wa majalisar dokokin kasar sunayen mutanen da za su zabi shugaban kasa daga ciki, bayan an nada shi a matsayin shugaban rikon kwarya na Sri Lanka bayan Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da ta nuna wa’adin dokar ta bacin  ta farko ta kare ko kuma an janye ta.

Duk da cewa ba a fayyace abin da sabuwar dokar ta kunsa ba, amma a baya gwamnatin kasar kan yi amfani da dokar ta baci wajen girke sojoji domin tsarewa da kulle mutane da kuma gudanar da bincike a gidaje da nufin murkushe masu zanga-zanga.