✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ayyana dokar hana fita a Borno

An kashe mutane 19 yayin da ‘yan sanda suka tabbatar da mutuwar mutum 16.

An kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a jihar Borno a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Nahum Kenneth Daso ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Daso ya ce an sanya dokar hana fitar ce biyo bayan tashin bom da aka samu ranar Laraba.

Aminiya ta ruwaito yadda wani bam ya tashi a wani wajen sayar da shayi a Borno a jajibirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar.

Kodayake majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa, an kashe mutane 19, amma ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 16.

A cikin sanarwar da ya fitar, kakakin ’yan sandan ya ce an ɗauki matakin hakan ne domin tabbatar da tsaro bisa ga la’akari da halin da ake ciki.

“Bisa la’akari da aikin da tsarin dokar ƙasa ya ba rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da jami’an tsaro da abin ya shafa na kiyaye doka da oda a jihar.

“Ku dai kuna sane da lamarin da ya faru a garin Kamari wanda ya kasance an samu tashin bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane 16 yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka suke jinya a asibitocin gwamnati daban-daban a jihar,” a cewar Daso.