✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban rikon karamar hukumar Gombe, Ali Ashaka ya rasu

Shugaban ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Allah Ya yi wa Shugaban riko na Karamar Hukumar Gombe, Alhaji Aliyu Usman Haruna (Ashaka) rasuwa, bayan fama da rashin lafiya.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Aliyu Usman Haruna shi ne shugaban Kungiyar Shugabanin Kananan Hukumomin na Jihar Gombe.

Ya rasu a wani asibiti a kasar Masar, yana da shekara 58 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Babban daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli ne ya sanar cewa gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya kadu da labarin rasuwar.

Ya ce rashin ba iya Gombe ce za ta yi ba, ba har da Nijeriya baki daya, domi kuwa marigayi Ashaka jajirtacce ne, mai amana da biyayya, wanda ya ce mutuwar ta taba shi sosai.

Ali Ashaka ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya shida.