Shugaban kungiyar Yarbawa zalla ta OPC Gani Adams, Aare Ona Kakanfo, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma da su bai wa al’ummarsu izinin mallakar lasisin bindiga.
Gani Adams ya bayyana haka ne a yayin da yake cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma, a cikin wani sako da ya fitar a ranar Laraba 26 ga watan Augustan 2020.
- Rikicin ‘yan Shi’a da ‘yan sanda ya yi ajalin mutum biyu a Kaduna
- Yadda manoman shinkafa suka yi asarar Naira biliyan 1
Sanarwar mai dauke da sa hannun Atoloye Aare Ona Kakanfo na lardin Yarbawa, Babajide Tanimowo, ta yi ikirarin samun labarin shigowar ‘yan ta’addan Fulani makiyaya zuwa yankin Kudu maso Yamma.
Ya yi zargin ce Fulanin masu alaka da kungiyar ISIS suna nan a yankin Jihar Neja a shiyar lardin Ibaruba da kuma yankin Oke Ogun a Jihar Oyo.
Ya ce sun gano makamai da manyan babura guda 500 na ‘yan ta’addar a kan hanyar Lusada da ba a amfani da ita wacce take isa zuwa Jihar Sakkwato daga garin Igbo-ora a Jihar Oyo.
Wannan ne ya sanya OPC ta bukaci gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma da na jihohin Kogi da Kwara da su yi koyi da Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, su umarci jama’arsu su mallaki lasisin bindiga domin kare kansu daga ‘yan ta’adda.
“Shugaba Buhari ka tashi tsaye, ka hana kashe-kashe a Kudancin Jihar Kaduna, da jihohin Filato da Taraba da sauransu.
“Yunkurin al’ummar Yarbawa domin samar da tsaro a yankinsu ya wuce samar da kungiyar Amotekun ko kuma duk wata kungiyar kare kai; Yunkuri ne na kare yankinmu na gado da al’adunmu abin faharinmu.
“Tun a shekarar 1991 al’ummar mu ke hankoron ganin an ba su damar mallakar albarkatun yankinsu da kuma sauya salon tsarin mulkin kasa domin samar da adalci ga kowane bangare; Al’ummarmu ta gaji da rufe baki ana ci gaba da zalumtar ta”, inji sanarwar.