✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban NNPC ba ya min biyayya- Ministan Albarkatun Man Fetur

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Dokta Ibe Kachikwu, ya zargi Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na NNPC, Dokta Maikanti Baru da rashin biyayya da musgunawa.…

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Dokta Ibe Kachikwu, ya zargi Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na NNPC, Dokta Maikanti Baru da rashin biyayya da musgunawa.
Kachikwu ya yi zargin ne a wasikar da ya aike wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wacce ke dauke da kwanan watan ranar 30 ga watan Agustan shekarar 2017 wacce aka rika yada ta a kafar sada zumunta jiya.
Kamfanin mai na NNPC ya shelanta yi wa ma’aikatansa garambawul tare da nada manyan mukamai a ranar 29 ga watan Agustan shekarar 2017.
Ministan wanda ya jagoranci taron shugabannin kamfanin ya yi korafin a wasikarsa cewa babban manajan daraktan kamfanin bai sanar da shugabbanin kamfanin  aniyarsa ta yi wa ma’aikatan kamfanin garambawul ba.