✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Nicaragua ya zabi matarsa ta zama Mataimakiyarsa

Shugaban kasar Nicaragua Mista Daniel Ortega ya zabi matarsa domin ta zama Mataimakiyarsa a zaben Shugaban kasar da ya tsaya a karo na uku.Gidan rediyon…

Shugaban kasar Nicaragua Mista Daniel Ortega ya zabi matarsa domin ta zama Mataimakiyarsa a zaben Shugaban kasar da ya tsaya a karo na uku.
Gidan rediyon BBC wanda ya ruwaito labarin ya ce dama matar tasa, Rosario Murillo, tana da babban mukami a kasar domin ita ce mai magana da yawun Shugaban kasar, kuma ana yi mata kallon wadda take taya Shugaban gudanar da mulkin kasar.
Rahotannin sun ce kusan kullum sai ta bayyana a gidan talabijin din kasar domin bayar da bayani a kan wasu shirye-shiryenta.
Shi kuwa Shugaba Ortega ba kasafai yake fitowa bainar jama’a ba a baya-bayan nan.
Wadansu dai na sukar matar da mijinta kan wannan batu, suna cewa sun mayar da mulkin kasar kamar gadon gidansu.
Misis Rosario Murillo, wacce ta haifa wa Shugaban kasar ’ya’ya bakwai, ta kware wajen magana da harshen Ingilishi da Faransanci, baya ga kasancewarta fitacciyar marubuciyar wakoki.
Misia Murillo ta kuma yi fice wajen sanya tufafin kawa da gwala-gwalai wadanda aka saba gani a shekarun 1960.
Mista Ortega, mai shekara 70, tsohon dan yakin sunkuru da ya kafa gwamnati a sakamakon juyin juya-halin Sandinista da ya rusa mulkin iyalan Somoza, wadanda suka mulki kasar na tsawon shekara 40.
Sandanistas wadanda suka samu tasiri daga kasar Kyuba sun kwace mulki ne a 1979, sai dai jam’iyyar ta fadi a zaben 1990, amma sai Mista Ortega ya dawo gadon mulki bayan samun nasara a zaben shekarar 2007.