✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban mawakan Kaduna, Sani Chairman Maidangiwa, ya rasu

Allah Ya yi wa Shugaban Mawakan Kaduna, Sani Chairman Maidangiwa rasuwa.

Allah Ya yi wa Shugaban Kungiyar Mawakan Kaduna, Malam Sani Chairman Maidangiwa rasuwa.

Shugaban Masana’antar Fim ta Kaduna, wato Kadawood, Nura MC Khan ne ya sanar da hakan ga Aminiya.

Ya ce, “Allah Ya yi wa Shugaban Kungiyar Mawakan Jihar Kaduna Sani Chairman Maidangiwa rasuwa. Allah Ya jikan sa.”

Aminiya ta samu labarin cewa mawakin ya rasu ne a daren Talata, kuma an yi masa jana’iza da safiyar Laraba kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.