✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Masu Rinjaye da na Marasa Rinjaye a Majalisar Dattijai sun ajiye mukamansu

Sun sauka daga mukaman ne bayan sauya sheka daga jam’iyyunsu na baya

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattijai, Sanata Yahaya Abdullahi, da na Marasa Rinjaye,  Enyinnaya Abaribeya  sun sanar da ajiye mukamansu a majalisar  bayan sauya sheka daga jam’iyyunsu.

Tsofaffin shugabannin biyu dai sun bayyana dangwarar da jam’iyunsu na baya a matsayin dalilan ajiye matsayin nasu, a takardar da suka mika ga Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, wacce kuma aka karanta a zaman majalisar na ranar Talata.

Sanata Ahmad Lawan ya ce Abaribe dai ya fice daga tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ne zuwa APGA, yayin da Sanata Abdullahi kuma ya koma PDP, daga tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.

Hakan dai na nufin yanzu jam’iyar APGA kamar YPP na da wakili guda a zauren majalisar.

A nasa bangaren, tsohon Shugaban Masu Rinjaye ya ce ya bar jam’iyyar APC ne saboda jefa ta a aljihu da yake zargin Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da yi, da kuma yin biris da matsalolin da take fuskanta da shugabancinta na kasa ya yi.

“Ba zan iya ci gaba da kasancewa da gwamnatin da al’ummata ke kuka da ita ba, bayan ganin idona suna fama da wahala, an jefa su a kangin talauci, ga kuma uwa uba rashin shugabanci na gari. Haka ne ya sanya na koma jam’iyyar PDP domin hada hannu da masu kishin kasa, wadanda kuma ba sa goyon bayan rashin kwarewa ko keta iyakokin dimukuradiyya” inji Sanata Yahaya.

A hannu guda, shi ma Sanata Adamu Alero da ke wakiltar mazabar Kebbi ta Tsakiya a Majalisar, ya sauya sheka zuwa PDP daga tsohuwar jam’iyyarsa ta APC, kamar dai yadda shi ma ya bayyana a takardar da  Shugaban majalisar ya karanta a zaman na ranar Talata.