Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattijai, Sanata Yahaya Abdullahi, da na Marasa Rinjaye, Enyinnaya Abaribeya sun sanar da ajiye mukamansu a majalisar bayan sauya sheka daga jam’iyyunsu.
Tsofaffin shugabannin biyu dai sun bayyana dangwarar da jam’iyunsu na baya a matsayin dalilan ajiye matsayin nasu, a takardar da suka mika ga Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, wacce kuma aka karanta a zaman majalisar na ranar Talata.
- Buhari ya gana da Gwamnonin APC kan zabar Mataimakin Tinubu
- An kashe matashi saboda budurwa a Kaduna
Sanata Ahmad Lawan ya ce Abaribe dai ya fice daga tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ne zuwa APGA, yayin da Sanata Abdullahi kuma ya koma PDP, daga tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.
Hakan dai na nufin yanzu jam’iyar APGA kamar YPP na da wakili guda a zauren majalisar.
A nasa bangaren, tsohon Shugaban Masu Rinjaye ya ce ya bar jam’iyyar APC ne saboda jefa ta a aljihu da yake zargin Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da yi, da kuma yin biris da matsalolin da take fuskanta da shugabancinta na kasa ya yi.
“Ba zan iya ci gaba da kasancewa da gwamnatin da al’ummata ke kuka da ita ba, bayan ganin idona suna fama da wahala, an jefa su a kangin talauci, ga kuma uwa uba rashin shugabanci na gari. Haka ne ya sanya na koma jam’iyyar PDP domin hada hannu da masu kishin kasa, wadanda kuma ba sa goyon bayan rashin kwarewa ko keta iyakokin dimukuradiyya” inji Sanata Yahaya.
A hannu guda, shi ma Sanata Adamu Alero da ke wakiltar mazabar Kebbi ta Tsakiya a Majalisar, ya sauya sheka zuwa PDP daga tsohuwar jam’iyyarsa ta APC, kamar dai yadda shi ma ya bayyana a takardar da Shugaban majalisar ya karanta a zaman na ranar Talata.