Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya sauka daga mukaminsa bayan sojoji sun tsare shi tare da Firaminista Boubou Cisse.
Shugaban ya kuma sanar da rushe gwamnatinsa da Majalisar Ministocin kasar a sanarwar da ya yi ta talbijin bayan sojojin sun yi awon gaba da su zuwa bariki a ranar Talata.
“Ba na so a zubar da jini domin in ci gaba da zama a kan mulki”, inji shi.
Tun da farko a ranar wasu fusatattun sojoji sun kwace iko a babban barikin Kati inda suka tsare kwamandoji da manyan hafsoshi.
Boren da tsare shugabannin kasar da sojojin suka yi ya sha kakkausar suka daga gwamnatoci da hukumomin kasashen duniya.
Sojojin na bore ne a kan matsalar albashi da rashin gamsuwa da kamun ludayin gwamnatin tsohon shugaban musamman a yakin da take yi da mayaka masu ikirarin Jihadi.
Ko kafin nan Gwamantin Mista Keita na fama da masu zanga-zangar kin jininta saboda rashin katabus a kawar da matsalar mayakan.
Masu zanga-zangar da suka banka wa Ofishin Ministan Shari’a wuta a birnin Bamako sun fusata da abun da suka kira kara durkushewar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa da suka dabaibaye kasar.
“Idan wannan shi ne abun da wasu daga cikin dakarun gwamnati suka zaba a matsayin shiga tsakani domin kawo maslaha, to ba ni da zabi.
“Ni babu wanda zan tsana domin kaunar kasata ba za ta bari har in tsani wani ba. Allah Ya yi mana albarka”, inji Mista Keita, wanda ya fara wa’adin mulkinsa na biyu bayan a shekarar 2018.