Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, David Sassoli, ya rasu da sanyin safiyar Talata bayan ya shafe sama da mako biyu a kwance a asibiti.
Kakakinsa, Roberto Cuillo, ya ce David Sassoli, wanda tsohon fitaccen dan jarida ne, ya rasu yana da shekara 65 sakamakon raunin garkuwar jikinsa da ya sa aka kwantar da shi a asibiti.
- Takarar Tinubu: Shugaba Buhari “ya shiga tsaka mai wuya”
- Afghanistan na bukatar kayan agajin Dala biliyan 5 a 2022 —MDD
Cuillo ya ce, “David Sassoli ya rasu da misalin 1.15 na dare, ranar 11 ga Janairu, 2022 a asibitin CRO da aka kwantar da shi a Aviano da ke kasar Italiya; nan gaba za a sanar da rana da kuma lokacin da za a yi jana’izarsa.”
A ranar Litinin ne Cuillo ya sanar da soke ziyarce-ziyarcen Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Marigayi David Sassoli, wanda aka kwantar da shi a asibiti tun a ranar 26 ga watan Disamban 2021.
Kafin nan, a watan Satumba ma ya shafe makonni a asibiti a sakamakon cutar Lamoniya.
Mambobin Majalisar Tarayyar Turai na da wa’adin shekara biyar, amma wa’adin shugabanta kuma rabin hakan ne.
Tuni dai Sassoli ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar kujerarsa, kafin mutuwa ta dauke shi.
Takaitaccen tarihin David Sassoli
An haifi David Sassoli ne a ranar 30 ga watan Mayu, 1956, a Florence na kasar Italiya.
Sassoli ya shafe shekara 30 yana aiki a matsayin dan jarida a kasarsa, inda ya yi aiki a gidan jarida; daga bisani ya koma aiki a bangaren talabijin har ya zama shahararren mai gabatar da shiri.
A shekarar 2009 Sassoli ya zama mamba a Majalisar Tarayyar Turai, ya kuma zama Shugaban Majalisar a 2019.
Ya rasu a ranar Talata, 11 ga watan Janairu, 2022, a yayin da yake shirin sake tsayawa takarar kujerarsa a karo na biyu.
A ranar Talata mai zuwa ne ake sa ran mambobin majalisar za su yi zagayen farko na zaben wanda zai maye gurbinsa.