Gwamnatin Ekiti ta ba da sanarwar rasuwar Shugaban Majalisar Dokokin jihar, Honarabul Funminiyi Afuye a ranar Laraba.
Sanarwar da ta fitar ta hannun Sakataren Yada Labarai ga gwamnan jihar, Mista Yinka Oyebode, ta ce marigayin ya rasu ne da yammacin Laraba a Asibitin Koyarwa na Jihar (EKSUTH), da ke Ado-Ekiti babban birnin jihar.
- Matashin da aka sace wa babura masu kafa uku ya kashe kansa
- Dalibai sun yi zanga-zangar rashin biyan albashin malamai
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa Atiku ya ce ’yan Arewa su zabi dan uwansu?
Ta ce Afuye ya cimma ajali ne sakamakon fama da bugun zuciya, kuma ya bar duniya yana da shekara 66.
Kafin rsuwarsa, tsohon Kwamishina ne a Ma’aikatar Yada Labarai ta jihar, kuma sau biyu yana zama mamba a Majalisar Dokokin jihar inda ya wakilci mazabar Ikere ta daya.
Bayanai sun ce ko a Lahadin da ta gabata, an ga Afuye a wajen bikin rantsar da Gwamna Biodun Oyebanji na jihar, kuma ya halarci zaman majalisa a Talatar da ta gabata.