Wasu da ake zargin fusatattun matasa ne daga garin Obbo-Aiyegunle a Jihar Kwara a ranar Talata sun kai hari a Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Ilejemeje da ke Jihar Ekiti da wasu mazauna garin kan rikicin fili.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa matasan da ake zargin sun harba bindiga don tsorata mazauna yankin.
An lalata tagogi da ƙofofin sakatariyar ƙaramar hukumar yayin da ma’aikatan ke gudu domin tsira da rayukansu.
Da yake magana kan harin, basaraken yankin Eleda na Eda-Oniyo, Oba Awodipo Awola, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun far wa wasu mutane, sakamakon haka aka kwantar da mutum ɗaya a asibiti.
Oba Awola ya ce lamarin ya haifar da ruɗani da fargaba a tsakanin al’ummarsa.
Ya buƙaci gwamnatin jihar da ta shiga tsakani domin sasanta rikicin, don kaucewa zubar da jinin waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.
Basaraken ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi ga al’umma domin hana ci gaba da kai hare-hare a yankin.
Da yake mayar da martani, shugaban Ƙaramar hukumar Ilejemeje a Ekiti, Mista Alaba Dada, ya bayyana kaɗuwarsa kan lamarin, inda ya ƙara da cewa an turo jami’an tsaro zuwa garin.