✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ɗaure malamin makaranta shekara 15 saboda yi wa ɗalibarsa fyaɗe

Oluwafemi a wani lokaci a shekarar 1999 a Ekiti, ya yi wa yarinyar fyaɗe lokacin tana ‘yar shekara 8.

Wata Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa wani malamin makaranta hukuncin ɗaurin shekara 15 saboda samunsa da laifin yi wa wata ƙaramar yarinya mai shekara takwas fyaɗe.

An ƙunshin tuhumar, malamin makarantar ya aikata laifin ne a shekarar 1999 a gidan su yarinyar da ke yankin Ikere a jihar ta Ekiti.

Tun a watan Agustan 2023 aka gurfanar da Oluwagbemi Alabi, mai shekara 45 a gaban kotun.

Wanda ake tuhumar, a cikin shaidarsa, ta ce: “Wanda aka yi wa fyaɗen ta ce malamina ne kuma maƙwabcinmu.

Ya riƙa taɓa nonona duk lokacin da ya zo ya koya mini karatu a gida, ban fahimci komai ba game da abin da yake yi sai da ya yi min fyaɗe a cikin falon gidanmu lokacin da mahaifiyata ta yi tafiya zuwa Legas ta bar ni da ƙanwata a gida.

“Ya cire tufafina ya yi amfani da shi wajen goge jini da maniyyi ya jefar da shi, daga baya na garzaya zuwa maƙwabtanmu ina kuka, sun ɗauka ina kewar mahaifiyata ne, amma ban gaya musu abin da ya faru ba.

“Bayan haka, na daina makaranta domin ba zan iya maida hankali ga karatuna ba. Ina jin tsoro duk lokacin da na gan shi a cikin aji.

“Sai a shekarar 2012 ne na sake cin karo da shi a shafin Facebook, ya aiko min da buƙatar abokantaka amma na ƙi.

“A shekarar 2023 kuma, ya fara tayar min da hankali, na kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro, inda aka ba ni shawarar da fita batunsa.

“Bayan haka, sai ya fara aika min da bidiyo da saƙonni masu tayar da hankali da ban haushi, yana tuna min mumunar lamarin da ya faru a baya. Da na kasa jurewa, sai na yanke shawarar ɗaukar matakin shari’a a kansa.”

A yayin da kotun ta nemi jin bahasin wanda ake zargin, ya amince da laifin da ake tuhumarsa da shi ba tare da wata fargaba ba.

Daga nan ne kuma alƙalin kotun, Mai shari’a Lekan Ogunmoye ya ce laifin da Alabi ya aikata na yin amfani da ƙarfi wajen haike wa ƙaramar yarinya babban laifi ne.

Daga nan ne kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 15 domin ya girbi abin da ya shuka.