Shugaban Kwamitin DCP Abba Kyari kan zargin almundahana, wato Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda Joseph Egbunike ya rasu a bakin aiki.
Wani dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa DIG Egbunike ya rasu ne bayan ya yanke jiki fadi a ofishinsa a ranar Talata.
Nan take aka garzaya da shi zuwa Asibitin Kasa da ke Abuja, inda likitoci suka tabbatar cewa rai ya yi halinsa.
DIG Joseph Egbunike shi ne mutumin da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kafa kan binciken zargin da ake wa Abba Kyari, shahararren dan sanda da a baya-bayan nan ya yi kaurin suna bisa zargin aikata miyagun ayyuka.
Kaifn a yi misi karin girma zuwa DIG a 2020, shi ne Shugaban Sashen Kudade na Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, daga baya aka mayar da shi ya jagoranci Sashen Binciken Manyan Laifuka a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Kasa (FCIID).
A shekarar da gabata ce Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali ya nada DIG Egbunike a matsayin shugaban kwamitin binciken zargin da ake wa Abba Kyari kan zargin damfara ta sama da Dala miliyan 1 wadda fitaccen dan damfara ta intane, Abbas Ramon, wato Hushpuppi, ya aikata.
Wakilinmu ya nemi samun karin bayani game da rasunar DIG Egbunike daga Mukaddashin Kakakin Rundanar ’Yan Sandan Najeirya, Olumuyiwa Adejobi, amma ya katse kiran.
Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto kuma bai amsa rubutaccen sakon da wakilinmu ya aike mishi ba.