✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Kenya ya dakatar da jami’an hukumar zaben da suka ki amincewa da nasararsa

Jami'an dai ba su amince da nasarar da ya samu ba tun da farko

Shugaban Kasar Kenya, Willam Ruto ya dakatar da jami’an hukumar zaben kasar (IEBC) su hudu, wadanda suka ja da sanarwar zaben da ya lashe a watan Agusta.

Matakin Shugaban ya fito fili a ranar Juma’a bayan da Majalisar Kasar ta bukaci William Ruto ya kafa kwamitin da zai binciki Kwamishinonin zaben hudu kan matsayin da suka dauka bayan zaben.

Jami’an hudu; Juliana Cherera da Justus Nyang’aya da Irene Masit da kuma Francis Wanderi sun nuna rashin gamsuwar su da lissafin kidayar kuri’ar da aka jefa, da cewa da akwai aringizo a ciki.

Ruto ya samu nasara da kaso 50.49 na jimlar kuri’un da aka kada yayin da abokin takararsa, Raila Odinga ya samu kaso 48.85 a  zaben.

Odinga ya kira matakin Ruto da cewa wani shiri ne na tafka magudi a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

“Abin a bayyane ya ke, Ruto ya soma kulle-kullen tafka magudi a zaben 2027 tun a shekarar 2022. Ba kuma zamu yarda hakan ta faru ba” in ji Odinga.

Jami’an hudu sun kira taron ‘yan jarida ne a inda suka bayyana matsayinsu na kin amincewa da sakamakon zaben, jim kadan bayan shugaban hukumar zaben ya sanar da nasarar ta Ruto.