✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Kasar Syria da matarsa sun kamu da COVID-19

Rabon da a ga Shguaba al-Assad a bainar jama'a tun a 2020.

Shugaban Kasar Syria Bashar al-Assad da mai dakinsa Asma sun harbu da cutar COVID-19.

Fadar Shguaban Kasar ta bayyana a ranar Litinin cewa bayan ganin alamun cutar ce Shugaba al-Assad da matar tasa suka yi gwajin.

“Bayan ganin alamun COVID-19 Shugaba al-Assad da matarsa Asma sun yi gwajin PCR kuma sakamakon ya nuna suna dauke da ita.

“Sai dai cutar ba ta yi tasiri sosai ko ta galabaitar da su ba,” inji sanarwar wadda ta ce za su rika aiki daga gida tare da killace kansu na kusan mako uku.

Kasar Syria wadda ta shekara 10 tana cikin yaki na da mutum 1,063 da cutar da kashe daga cikin 16,000 da suka kamu da ita a yankuna da ke karkashin ikon gwamnati.

%d bloggers like this: