Shugaban Kasar Senegal Macky Sall ya fara killace kansa bayan ya yi mu’amala da wani mutum da aka gano yana dauke da cutar coronavirus.
Kamuwar mutumin da cutar ta bayya ne bayan ganawarsa da Mista Sall a cewar Fadar Shugaban Kasar.
Gwamantin Senegal ta ce Shugaba Sall zai ci gaba da kasancewa a killace na tsawon mako biyu domin tabbatar da yanayin lafiyarsa.
Sanarwar da ofishin shugaban kasar ya fitar ta ce gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban kasar bai harbu da kwayar cutar ba, amma zai ci gaba da killace kansa a matsayin riga-kafi.
Ofisoshin ya yi kira ga ‘yan kasar su kwantar da hankalinsu tare da bin matakan kariya daga cutar.