Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu yana da shekara 55 a duniya.
Gwamnatin Burundi ta sanar da mutuwar Shugaba Pierre Nkurunziza bayan ya yi fama da bugun zuciya a daren Talata talata, 9 ga watan Yuni.
Mutuwar ta Nkurunziza mai shekara 55 na zuwa ne bayan zaben kasar na watan jiya da dan takarar jam’iyyarsa Evariste Ndayishimiye ya samu gagarumin rinjaye wanda zai maye gurbinsa a watan Agusta.
Gwamnatin kasar ta ce a ranar Asabar an kwantar da shugaban gadon asibiti bayan ya fara jin alamun rashin lafiya.
Ya kuma samu sauki daga baya amma sai a ranar Litinin ciwon bugun zuciya ya same shi, kuma kokarin da aka yi na ceto ransa ya faskara.