Akalla mutum 38 ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan yari a Kasar Burundi a ranar Talata.
Mataimakin Shugaban Kasar, Prosper Bazombanza, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce wasu mutum 69 sun ji rauni.
- Hotunan bikin bajekolin fina-finai a Saudiyya
- Buhari ya kori shugabannin kamfanin wutar lantarkin Abuja kan dauke wuta
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 4 na dare, inda wutar ta lalata wurare da dama na ginin gidan yarin.
Sai dai har yanzu ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba, wadda aka samu nasarar kashe ta, zalika babu wani bayani a hukumance kan lamarin.
Gidan yarin na birnin Gitega na dauke da fursunoni sama da 1,500, amma a watan Nuwamba adadin da ya zarce yawan fursunoni 400 da a tsare a gidan.
Yawancin fursunonin da ke gidan yarin maza ne amma kuma akwai bangaren mata.