Shugaban Kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye, ya kori dukkan Ministocinsa da aka gano suna da wasu ’yan mata ban da matansu na aure daga bakin aiki.
Ministan Tsaron Cikin Gida na kasar, Gervais Ndirakobuca ne ya sanar da daukar sabon matakin a matsayin wani yunkunrin gwamnati mai ci na tsaftace tarbiyya a kasar.
- ’Yan bindiga sun harbe mutum 19 suna tsaka da cin kasuwa a Sakkwato
- Amurka ta fara hawa teburin tattaunawa da ’yan Taliban
A cewar dokar, dukkan jami’in gwamnati mai aure da aka gano yana da ’yan mata ko kuyangu, zai iya fuskantar hukunci kora daga mukaminsa.
Wannan dai shi ne mataki na biyu irinsa na shirin tsaftace tarbiyyar kasar da marigayi Shugaban Kasa Pierre Nkurunziza ya kirkiro.
A watan Mayun 2017, Shugaba Nkurunziza, wanda cikakken mabiyin addinin Kiristanci ne ya rattaba hannu a kan wata doka da ta bukaci dukkan masu soyayya a kasar su yi aure kafin karshen watan Disamban shekarar, ko su fuskanci fushin hukuma.
A kasar Burundi dai, ana samun yawan karuwar mazan da ke yin soyayya da ’yan mata da yawa a lokaci guda tare da yi musu cikin shege.
“Muna so ’yan Burundi su fahimci cewa kowa na da alhakin tafiyar da akalar rayuwarsa, muna son mu sami tsafta a kasarmu,” kamar yadda Kakakin Ministan Tsaron na Burundi, Terence Ntahiraja, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.
Nkurunziza dai ya mutu a shekarar 2020, lamarin da ya kai Evariste ga karbar ragamar shugabancin kasar.